An yankewa wacce ta raba man fetur a taro hukuncin watanni 27 a gidan yari

An yankewa wacce ta raba man fetur a taro hukuncin watanni 27 a gidan yari

  • Kotu cikin gaggawa ta yanke hukunci kan matar da ta rabawa kawayenta jarkokin man fetur a wajen taro
  • Kotu ta ce matar ta biyar tarar sama da milyan daya ko ta kwashe shekaru biyu da wata biyu a gidan gyara hali
  • Gwamnatin jihar Legas ce ta shigar da matar kotu kan zargin jefa rayukan mutane cikin hadari

Kotun laifuka na musamman dake jihar Legas ta yankewa Ogbulu Chidinma Pearl hukuncin daurin watanni 27 a gidan gyara hali.

A ranar 4 ga Maris, Pearl ta raba jarkokin man fetur wa mahalarta taron bata sarauta a jihar.

Bidiyoyin taron sun yadu a kafafen ra'ayi sada zumunta.

A ranar Juma'a, Alkalin kotu, Kehinde Ogundare, ya kama ta da laifi kan dukkan laifukan da ake zarginta da su.

Kan laifin farko, ya yanke hukuncin watanni uku ko ta biya tarar N15,000.

Kara karanta wannan

Azumin Ramadan: Sarkin Musulmi ya yi gargadi kan kara farashin kayan masarufi

Kan laifi na biyu da na uku, an yanke mata hukuncin daurin shekaru biyu, ko kuma ta biya kudin tarar N1,000,000.

An yankewa wacce ta raba man fetur a taron hukuncin watanni 27 a gidan yari
An yankewa wacce ta raba man fetur a taron hukuncin watanni 27 a gidan yari
Asali: Instagram

Wahalar Mai: Anyi rabon jarkokin man fetur a wani bikin jihar Legas

Kwanaki goma da suka gabata Yayinda yan Najeriya ke fama da matsanancin wahalar man fetur, mun kawo muku rahoton cewa an yi rabon jarkokin mai matsayin kyautar halartar biki a jihar Legas.

A hotunan da bidiyon da wani @ThisIsKennys ya saki a shafinsa na Tuwita, an kan yadda aka lika hotunan wanda ke bikin a jikin jarkuna da sunan "Erelu Okin Foundation Installation Party.”

Kalli bidiyon bikin:

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: