Taron gangamin APC: An yi ram da masu sane 3 a cikin jama’a
1 - tsawon mintuna
- Jami'an tsaro sun yi ram da ƴan sane a dandalin gangamin zaɓen shuwagabannin jam'iyyar APC a Eagle Square dake Abuja
- Sun yi amfani da damar cunkoson da wakilan zaɓe ke yi a bakin kofa wajen kwace wayoyi da kuɗin mutane, jami'in tsaro ya bayyana
- A halin yanzu, an miƙa waɗanda ake zargin hedkwatar ƴan sanda don cigaba da bincikar lamarin
Jami'an tsaro sun damko mutane uku da ake zargin ƴan sane ne a dandalin gagarumin zaɓen shuwagabannin jam'iyyar APC bayan an kama su suna ƙwace wayoyi a bakin kofa, Daily Trust ta ruwaito.
Jami'in tsaron, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Asabar a Abuja, yadda waɗanda ake zargin suka yi amfani da damar cunkoson dake ƙofar shiga Eagle Square wajen kwace wayoyin mutane.
"Sun yi amfani da damar cunkoson da wakilan zaɓe ke yi a bakin kofa wajen kwace wayoyi da kuɗi.
"Abunda da ya faru shine, basu da masaniya game da yadda muka aje ƴan sandan da suka zura ido a kofar domin lura da shige da ficen wakilan zaɓe.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wannan shi ne takamaiman abunda ya faru, jami'in mu ya kama su bayan sun kwace wayoyin mutane," a cewarsa.
Jami'in mutsaron ya bayyana yadda aka miƙa waɗanda ake zargin hedkwatar ƴan sanda don cigaba da bincike, The Nation ta ruwaito.
Asali: Legit.ng
Tags: