Yanzu-yanzu: Abdullahi Adamu mukayi ittifakin ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC, Gwamna Sule

Yanzu-yanzu: Abdullahi Adamu mukayi ittifakin ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC, Gwamna Sule

  • Shugaban kwamitin yada labarai na taron gangamin jam'iyyar APC ya bayyana zabin Shugaba Buhari
  • Wasu yan takara kujeran shugabancin jam'iyyar da dama sun bayyana rashin jin dadinsu amma sun yi biyayya ga shugaba Buhari
  • Gobe Asabar za'a gudanar da taron gangamin jam'iyyar APC a farfajiyar Eagle Square dake Abuja

Abuja - Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya tabbatar da cewa jam'iyyar All Progressives Congress ta zabi tsohon gwamna, Abdullahi Adamu, matsayin wanda za'a zaba sabon shugabanta.

Sule ya bayyana hakan da yammacin Juma'a yayin hira a shirin Politics Today na tashar ChannelsTV.

Gwamnan wanda yayi magana kan shirye-shiryen da jam'iyyar ke yiwa taron gangamin gobe Asabar, ya ce dokar zabe ta amince da hakan.

Yace:

"Ittifaki na daya daga cikin zabi. Yana cikin kundin tsarin mulkinmu kuma bai sabawa dokar zabe ba."

Kara karanta wannan

Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da Abdullahi Adamu, mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamna Abdullahi Adamu
Yanzu-yanzu: Abdullahi Adamu mukayi ittifakin ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC, Gwamna Sule
Asali: Facebook

Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, shugaban kwamitin labaran taron gangamin APC

Gwamnan jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin Midiya na babban taron APC na ƙasa, Abdullahi Sule, ya yi bayanin abin da yasa gwamnoni suka amince da zaɓin Buhari.

Tribune Online ta rahoto gwamnan na cewa Shugaba Buhari na goyon bayan tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya zama shugaban APC na gaba.

A ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022, APC zata gudanar da babban taronta na ƙasa wanda zata zaɓi shugabanninta.

Da yake jawabi ga manema labarai game da shirin da kwamitinsa ya yi, Gwamna Sule ya ce masu shakku kan zabin Buhari sun amince ne saboda girmamawan da Buhari ke samu daga masu faɗa a ji.

Kara karanta wannan

Osinbajo: Duk Musulmin da ya zabi dan cocin RCCG munafikin Musulunci ne, MURIC

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng