Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC

Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC

Bisa zabin shugaba Muhammadu Buhari, ana kyautata zaton Sanata Abdullahi Adamu ne zai zama sabon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress APC.

Taron gangamin jam'iyyar, inda za'a fafata a zaben zai gudana ne ranar Asabar, 26 ga Maris, 2022.

A ranar Alhamis, Gwamnan jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin Midiya na babban taron APC na ƙasa, Abdullahi Sule, ya yi bayanin abin da yasa gwamnoni suka amince da zaɓin Buhari.

Legit.ng Hausa ta binciko muku wasu abubuwan da ya kamata ku sani game da wannan mutumi mai shekaru 76 da shugaba Buhari ya zaba ya ja ragamar APC zuwa zaben 2023:

1. Tsohon ma'aikacin Abacha ne

Bayan shiga siyasa a 1977 da kuma nasara a zaben majalisar da ta rubuta kundin tsarin mulkin Najeriya na jamhuriyya ta biyu (1978-1983).

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Abdullahi Adamu mukayi ittifakin ya zama sabon shugaban jam'iyyar APC, Gwamna Sule

Daga baya marigayi janar Sani Abacha ya nadashi majalisar shawara ta kasa a 1994.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A 1995, Abacha ya sake nadashi karamin ministan ayyuka da gidaje zuwa 1997

2. Daya daga cikin wadanda suka kafa PDP

Yayinda ya harkokin siyasa suka dawo a 1997, Abdullahi Adamu ya shiga jam'iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP).

Amma bayan shekara guda suka kafa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC
Maye: Abu 5 da ya kamata ku sani game da mutumin da Buhari ya zaba matsayin shugaban APC Hoto: Presidency
Asali: Facebook

3. Ya yi gwamnan jihar Nasarawa tsawon shekaru 8

Dawowar demokradiyya a 1999, Abdullahi Adamu ya zama gwamnan jihar Nasarawa bayan samun nasara a zabe.

Bayan karewar wa'adinsa na farko, ya sake takara a 2003 kuma yayi nasara.

4. Shekarunsa 11 a majalisa

Bayan sauka daga gwamna a 2007 da hutun shekaru hudu, Abdullahi Adamu ya koma majalisar dokokin tarayya wakiltar mazabar Nasarawa ta yamma a majalisar dattawa.

Kara karanta wannan

Ku sake bamu dama mu mulki kasar nan: Gwamnonin PDP sun roki yan Najeriya

Har yanzu yana kan kujerar.

5. Shekaru 44 a siyasa amma bai taba fadi zabe ba

Wannan babban nasara da Sanata Abdullahi Adamu ke alfahari da shi itace tun da ya shiga siyasa ba'a taba kada shi ba tun 1978.

Kwanakin baya yace:

"Daga 1978 zuwa yanzu, ban taba fadi wani zabe ba. Ni ne kusan mutumin karshe da ya bayyana niyyar takara da gangan nayi hakan."

Dalilin da yasa muka miƙa wuya ga ɗan takarar da Buhari ke kauna, shugaban kwamitin labaran taron gangamin APC

Gwamnan jihar Nasarawa kuma shugaban kwamitin Midiya na babban taron APC na ƙasa, Abdullahi Sule, ya yi bayanin abin da yasa gwamnoni suka amince da zaɓin Buhari.

Tribune Online ta rahoto gwamnan na cewa Shugaba Buhari na goyon bayan tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya zama shugaban APC na gaba.

A ranar Asabar 26 ga watan Maris, 2022, APC zata gudanar da babban taronta na ƙasa wanda zata zaɓi shugabanninta.

Kara karanta wannan

Taron gangamin APC: Gobe Juma'a muke shirin sakin sunayen wadanda muka zaba, Ahmad Lawan

Da yake jawabi ga manema labarai game da shirin da kwamitinsa ya yi, Gwamna Sule ya ce masu shakku kan zabin Buhari sun amince ne saboda girmamawan da Buhari ke samu daga masu faɗa a ji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng