Zan nemi takarar shugabancin gida na, Ministan Buhari ya yi tsokaci kan takara a 2023
- Ministan ayyuka da gidaje a Najeriya, Babatunde Fashola, ya ce babu takarar da zai fito a 2023 sai ta shugabancin gidansa
- Ƙungiyoyi da dama sun jima suna kira ga Fashola ya shiga tseren shugaban kasa, amma ya ce matarsa da 'ya'yansa na can suna jiransa
- A cewarsa da zaran wa'adin mulkin su ya ƙare a 2023, zai koma gida a jihar Legas ya huta
Abuja - Ministan ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola, yace ya shiga takarar shugaban ƙasa amma na gidansa.
Mai taimakawa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kan harkokin Midiya, Tolu Ogunlesi, shi ne ya bayyana kalaman Ministan a wani rubutu a shafinsa na Twitter.
Ministan ya yi wannan furucin ne lokacin da manema labarai suka tambaye shi game da shirin da yake yi yayin da zaɓen 2023 ke gabatowa.
Da yake ba su amsa, Fashola ya ce:
"Ina neman takarar shugaba amma a gida na, Legas zan koma, matata da 'ya'ya na na can suna jiran shugaban su. Dukkan ma su neman takara ina musu fatan Alkhairi."
A kwanakin baya, yan Najeriya sun yaɗa jita-jitar cewa tsohon gwamnan jihar Legas ɗin zai shiga tseren takarar shugaban ƙasa a 2023.
Wasu ƙungiyoyin masoya sun fara karaɗe sassan Najeriya da yaƙin neman zaɓen Ministan, inda suka rinka kira gare shi da ya fito takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya.
Amma Ministan ya musanta alaƙa da irin waɗan nan ƙungiyoyi dake goyon bayan cewa ya fito takara.
Fashola ya maida hankali kan sauke nauyin dake kansa
Hadimin ministan, Hakeem Bello, ya bayyana cewa Fashola ya maida hankali ne wajen sauke nauyin dake kan ma'aikatarsa kuma ba za'a raba masa hankali ba.
A jawabinsa ya ce:
"Mai girma Minista ya maida hankalinsa kacokan kan jagorantar tawagarsa na ma'aikatar ayyuka da gidaje domin sauke nauyin da shugaba Buhari ya ɗora musu."
A wani labarin kuma Gwamna a Najeriya ya kori ma'aikata sama da 500 daga aiki, sun fantsama zanga-zanga
Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya amince da korar ma'aikata 513 daga bakin aiki waɗan da ke sashin harkokin wasanni.
A wani kundi mai ɗauke da sanarwan korar ma'aikatan, gwamnan ya ce ya ɗauki wannan matakin domin garambawul ga sashin.
Asali: Legit.ng