Dinbin mutane za su rasa aikin yi yayin da Naira ta kara durkushewa kasa a kasuwar canji
- Darajar kudin Najeriya yana kara yin kasa a kasuwar canji, abin yana kara jagwalgwalewa kullum
- Wannan matsala da ake fuskanta a yau ta na da mummunan hadari ga tattalin arzikin Najeriya
- Wadanda suka dogara da Dala domin su shigo da kaya daga ketare za su rasa inda za su sa kansu kenan
Jaridar Punch a wani rahoto da ta fitar, ta bayyana cewa karyewar Naira zai iya yin sanadiyyar da mutane masu yawa za su rasa hanyar cin abincinsu.
Maganar da ake yi a ranar Larabar nan shi ne Dalar Amurka 1 ta kai N590 a wajen ‘yan canji.
Kungiyar Manufacturers Association of Nigeria ta masu kere-kere a kasar nan ta ce jama’a za su rasa aikinsu a bangaren kere-kere da sauran harkoki.
Rahoton ya ce an tashi aiki a ranar Talata, 22 ga watan Maris 2022 yayin da Dala ta kai N585. Dalar £1 ta na N785. Abin ya kara muni ne a makon nan.
Sabon tsarin CBN
Hakan na zuwa ne kusan watanni takwas bayan babban bankin kasar na CBN ya dakatar da saida Dalar waje ga ‘yan canji watau Bureau de Change.
Karancin Dala a bankuna ya jawo aka tilastawa mutane kashe $20 rak a duk wata idan za ayi cefane ta kafar yanar gizo, kuma abin na ta dada cabewa.
Masu kere-kere sun shiga uku
Masu mu’amala da kudin kasar waje sun ce idan mutum ya nemi Dala a banki saboda zai je kasar waje, da wahala ya samu ko da rabin abin da yake bukata.
Rahoto ya nuna wadanda suke bangaren kere-kere sun fi kokawa shan wahala da halin da ake ciki. Masu shigo da kaya daga ketare ba su da kudin yin sayayya.
Bola Adefila ya nemi $425, 000 domin ya shigo da kaya daga kasar waje, amma sai bankin CBN suka ce abin da zai iya samu a hannunsu shi ne $210 kurum.
Abin da wannan ke nufi shi ne kamfanoni za su zama ba su da kayan aikin da suka dogara da su.
Lokacin zabe ya karaso, za a karya Naira?
Wata majiya ta shaidawa jaridar cewa yayin da zabe ya gabato, wahalar Dala za ta karu domin ‘yan siyasar Najeriya na kokarin tattara kudin kasar waje.
Bismarck Rewane wanda shi ne shugaban kamfanin Financial Derivatives Company ya yi hasashe cewa dole CBN zai karya darajar Naira karshen 2022.
‘Yan siyasa za su rika neman kudin da za su kashe ido rufe yayin da aka shigo lokacin zabe.
Asali: Legit.ng