Da duminsa: Gwamnonin APC sun gana da Shugaba Buhari a Abuja

Da duminsa: Gwamnonin APC sun gana da Shugaba Buhari a Abuja

  • Yayinda ake shirin taron gangamin jam'iyyar APC, Shugaba Buhari ya zanna da gwamnonin jam'iyyar
  • Rahotanni sun nuna cewa an samu rabuwar kai tsakanin gwamnonin kan wanda zai zama sabon shugaban jam'iyyar
  • Akalla mutum shida cikin yan takaran sun ce ba zasu janyewa Sanata Abdullahi Adamu ba

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka ya shiga ganawa da gwamnonin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaban kungiyar gwamnonin jam'iyyar APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, ya jagoranci gwamnonin zuwa zaman.

Wannan ya biyo bayan barakar da aka samu tsakanin gwamnonin APC kan wanda zai zama sabon shugaban jam'iyyar.

Hadimin Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmed, ya bayyana hakan a shafinsa na Tuwita.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC: Duk wanda Buhari ya zaba a taron gangamin shi za mu marawa baya

Gwamnonin APC
Da duminsa: Gwamnonin APC sun shiga ganawa da Buhari a Abuja Hotuna: Tolani Ali
Asali: Facebook

Gwamnonin APC
Da duminsa: Gwamnonin APC sun shiga ganawa da Buhari a Abuja Hotuna: Tolani Ali
Asali: Facebook

Da duminsa: Gwamnonin APC sun shiga ganawa da Buhari a Abuja
Da duminsa: Gwamnonin APC sun shiga ganawa da Buhari a Abuja
Asali: Facebook

Gwamna Buni ga masu sukar APC: Taron gangami ne a gabanmu, ba ta kowa muke ba

Shugaban kwamitin tsare-tsare na APC, Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyarsu ta mayar da hankali kan taron gangami ne, kuma ba ta da lokacin sauraran kafafen yada labarai ko kuma masu wasa da hankalinta, inji rahoton PM News.

Buni wanda ya kasance maudu'in cece-kuce a makonnin da suka gabata biyo bayan rade-radin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kore shi daga mukaminsa, ya ci gaba da cewa jam’iyyar ba za ta lamunci duk wani nau’in raba hankali a cikinta ba.

Ya bayyana hakan ne ta wata sanarwa da kakakinsa, Mamman Mohammed ya rabawa manema labarai a ranar Laraba, 23 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng