Innalillahi: An rasa rai 1 yayin da tankar mai ta yi arangama da tirela a Kano
- An rasa ran wani direban kamfanin Julisu Berger mai suna Aminu Dakatsalle a wani hatsari da ya ritsa da shi
- Motar kamfanin Julius Berger ta ci karo da tankar mai ta kamfanin Mege inda suka kama da wuta baki daya
- Mummunan lamarin ya faru ne a garin Chiromawa da ke kan titin Zaria zuwa Kano, an mika gawar direban asibiti
Kano - Mutum daya ya rasa rayuwarsa bayan wata motar tirela ta kamfanin Julius Berger Construction ta yi karo da wata tankar mai na kamfanin mai na Mege a garin Chiromawa da ke kan hanyar Zaria a Kano.
Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin da ya kai ga barkewar gobara da ta lakume motocin biyu, ta kama da wani direban kamfanin Julius Berger mai shekaru 40, mai suna Aminu Dakatsalle, wanda aka ceto shi a sume kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.
A yayin tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce tankar man da ke dauke da litar man PMS (man fetur) kimanin lita 60,000 ta lalace a kan hanyar Zariya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce tirelar kamfanin Julius Berger Construction mai lamba ENG 879 XB ta kutsa cikin motar dakon man fetur wanda hakan yasa suka kama da wuta, Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma kara da cewa musabbabin faruwar lamarin ya faru ne sakamakon rashin tsaro da aka samu, kuma an mika gawar marigayin ga jami’in ‘yan sanda na shiyyar Garun Malam.
Kano: Yadda Alkali Aminu Gabari ya karbi cin hancin zunzurutun kudi daga mai korafi
A wani labari na daban, wani babban alkalin jihar Kano, Aminu Gabari, an zarge shi da tilasta wa wani mai kara a wata kara da ke gaban kotunsa biyan kudi N400,000 a asusunsa a matsayin cin hanci.
Gabari ya yi kaurin suna wajen daurewa da kuma sanya wasu tsauraran sharuddan belin ga masu sukar gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.
Daily Nigerian ta tattaro cewa korafe-korafe da ke fitowa daga gidan gwamnatin Kano a koda yaushe ana shigar da su tare da gurfanar da su a gaban kotun sa, wanda hakan ya sabawa sashe na 107 (4)(5)(6) na dokar shari’a ta gwamnati, ACJL.
Dokar ta tanadi cewa alkalai a kotunan da ake shigar da kararraki kai tsaye bai kamata su zama wadanda za su yi shari'a ba sai dai kawai su gane laifin da aka aikata sannan su mika lamarin ga wani alkali.
Asali: Legit.ng