Masoyin ɗan siyasa ya mutu yana tsaka da murnar sauya shekar Uban Gidansa zuwa PDP a Abuja

Masoyin ɗan siyasa ya mutu yana tsaka da murnar sauya shekar Uban Gidansa zuwa PDP a Abuja

  • Wani masoyi ɗan gani kasheni na shugaban karamar hukuma a Abuja ya rasa rayuwarsa sanadiyyar hatsarin mota
  • Mutumin ya rasu ne yayin da suke tsaka da murnar sauya shekar Uban Gidansa Ciyaman na Gwagwalada daga APC zuwa PDP
  • Sauran mutum uku da suke cikin motar suna kwance a Asibiti, Mamacin kuma an masa jana'iza yadda musulunci ya koyar

Abuja - Wani magoyin baya kuma ɗan a mutun shugaban ƙaramar hukumar Gwagwalada a babban birnin tarayya Abuja, ya rasa rayuwarsa a hatsarin Mota.

Daily Trust ta rahoto cewa mutumin mai suna Awwal Idris, ya rasu ne yana tsaka da murnanr sauya shekar Uban gidansa Ciyaman, Alhaji Adamu Mustapha, daga APC zuwa PDP.

Tutar PDP
Masoyin ɗan siyasa ya mutu yana tsaka da murnar sauya shekar Uban Gidansa zuwa PDP a Abuja Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Rahoto ya tabbatar da cewa ragowar mutum uku dake tare da Mamacin a cikin Motar, yanzu haka suna kwance a wani Asibitin kuɗi dake Gwagwalada, Abuja.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Tsaro ya tabarbare a Imo, Buhari ya ce a tura karin jami'ai da makamai

Lamarin ya auku ranar Asabar da misalin ƙarfe 11:00 lokacin da tawagar Ciyaman din ke kan hanyar zuwa gundumar Dobi, inda zai tabbatar da sauya sheƙarsa a hukumance ta hannun shugaban PDP na Dobi, Abubakar Sarki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yadda mutumin ya rasa rayuwarsa a hatsarin

Bayanan da muka samu sun nuna mana cewa Motar da suke ciki ta sauka daga kan titi kuma ta wuntsila sannan ta dira a cikin hanyar ruwa dake bakin titin.

Bisa haka ne, Idris ya rasa rayuwarsa nan take a inda hatsarin ya auku, sauran kuma aka garzaya da su Asibitin domin kula da lafiyarsu.

Shugaban jam'iyyar PDP na karamar hukumar Gwagwalada, Alhaji Yunusa Abdullahi, ya tabbatar da faruwar hatsarin ga manema labarai ta wayar Salula.

Ya ce Mamacin, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Leda, inda Ciyaman na Gwagwalada ya fito, an masa jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.

Kara karanta wannan

Rikici gabanin taron gangamin APC: Kujerar shugabancin jam'iyya ta raba kan Sanatoci

A wani labarin kuma Yadda wani ɗan kasuwa ya halaka yan bindigan da suka yi garkuwa da shi, ya dawo gida lami lafiya

Wani ɗan kasuwa a Ondo ya yi jarumta a sansanin yan bindiga ya kashe mutum biyu yayin da bacci ya ɗauke su.

Bayanai sun nuna cewa mutumin ya yi kamar yana bacci mai nauyi, suma suka kwanta sai ya tashi ya ɗauki makamansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262