Zamu kashe tsutsar ciki na daliban Najeriya milyan daya, Hajiya Sadiya Farouq

Zamu kashe tsutsar ciki na daliban Najeriya milyan daya, Hajiya Sadiya Farouq

  • Gwamnatin tarayya na shirin fara baiwa daliban makarantun firamare maganin kashe tsutsar ciki
  • Ma'aikatar jin kai ta ce idan aka kashe tsutsotsin, daliban zasu kara lafiya kuma kwakwalwarsu zasu fi aiki
  • Daliban da zasu amfana da wannan shirin sun hada da wadanda gwamnati ke baiwa abinci da wadanda basu baiwa

Abuja - Ma'aikatar tallafi da jin kai ta bayyana cewa zata baiwa daliban makarantun firamare guda milyan daya maganin kashe tsutsar ciki don inganta lafiyarsu.

Shugaban shirin NSIP, Dr Umar Bindir, ya bayyana hakan a zaman shirye-shirye na tsawon kwana biyar dake gudana a birnin tarayya Abuja ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labarai NAN yace daya daga cikin manufofin zaman shine samar da kayayyakin kashe tsutsar cikin dalibai.

Kara karanta wannan

Rashin wutar lantarki ce matsala mafi girma ga cigabar kasar nan, Tinubu

Hajiya Sadiya Farouq
Zamu kashe tsutsar ciki na daliban Najeriya milyan daya, Hajiya Sadiya Farouq Hoto: FMHDS
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mr Bindir, wanda ya samu wakilcin mataimakiyar diraktar shirye-shirye, bincike da lissafe-lissafe a ma'aikatar, Safiya Sani, ya bayyana muhimmancin kashe tsutsar cikin don inganta lafiyansu.

Yace:

"Yadda muke basu abinci, akwai bukatar kashe tsutsotsin cikinsu saboda abinda ya rika aiki a jikinsu sosai don kara musu lafiya."
"Zamu rika wannan akai-akai saboda da yiwuwan an sawa wasu kayan abinci sinadarai ko kuma akwai tsutsa cikinsu. Idan muka kashe tsutsotsin, zasu kara lafiya kuma kwakwalwarsu zasu fi aiki."

Bindir yace yan ajin firamare 1 zuwa 6 za'a baiwa maganin, musamman yan makarantun gwamnati.

N-Power: Gwamnatin Tarayya za ta gwangwaje matasa 300, 000 da kudin jari inji Minista

Gwamnatin Najeriya ta ce ta shigo da wani tsari domin yaye dubban matasan da ba su da aikin yi, wadanda suke kammala shirin nan na N-Power.

Kara karanta wannan

Kwastam Ta Kama Motar Ɗangote Makare Da Buhun Haramtaciyyar Shinkafar Waje 250

Jaridar Premium Times ta kawo rahoto cewa gwamnati ta fito da tsari na musamman da zai taimakawa wadannan matasan da jari na fara kasuwanci.

Ministar bada agaji da tallafin gaggawa, Sadiya Umar Farouq ta bada wannan albishir a ranar Alhamis, 17 ga watan Fubrairu 2022 ga wadannan matasan.

A cewar Ministar, tsarin da aka zo da shi ga masu shirin barin aikin N-Power zai kunshi horaswa na musamman a bangarori dabam-dabam na samun kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng