Kotu ta sake ba Sowore gaskiya, ta ci DSS tara saboda cafke ‘Dan gwagwarmaya tun 2019

Kotu ta sake ba Sowore gaskiya, ta ci DSS tara saboda cafke ‘Dan gwagwarmaya tun 2019

  • Babban kotun tarayya na garin Abuja ya kammala sauraron shari’ar Omoyele Sowore da jami’an DSS
  • Alkali ya umarci hukumar tsaron na fararen kaya su biya Sowore kudi N1m a dalilin tsare shi a 2019
  • Hukuncin Obiora Egwuatu yana nufin kotu ta ba jami’an tsaro rashin gaskiya a dadaddiyar shari’ar

Abuja - Babban kotun tarayya da ke zama a garin Abuja, ta zartar da hukunci a game da cafke Omoyele Sowore da jami’an DSS suka yi tun a shekarar 2019.

Jaridar The Cable ta kawo rahoto a ranar Litinin, 21 ga watan Maris 2022 cewa Alkali ya ce kama wannan ‘dan gwagwarmaya da aka yi, ya sabawa dokar kasa.

A watan Agustan 2019 ne jami’an DSS masu fararen kaya suka yi ram da Sowore. Duk da cewa wasu kotu sun ce a bada belinsa, sai aka cigaba da tsare shi.

Kara karanta wannan

EFCC ta yi nasara, kotu ta raba tsohon babban soja da matarsa da dukiyarsu har abada

Wannan ya sa Yele Sowore ya shigar da kara a gaban kotu, ya na neman hakkinsa na kara watanni biyu da ya yi a tsare, har ya bukaci DSS ta biya shi N500m.

Lauyoyi sun je kotu

Lauyoyin da suka tsayawa Sowore sun roki kotu ta tursasawa jami’an tsaro su biya wadannan makudan kudi saboda an ci masa zarafi, an toye masa hakkinsa.

Sowore
Mista Yele Sowore Hoto: @Nigeria-Diaspora-International-Movement
Asali: Facebook

A cewar lauyoyin, tsare wannan mutum da aka yi ya zama cin karo da damar da dokar kasa ta ba shi na neman lafiya, kafa kungiya, shari’a a kotu da zirga-zirga.

An yi ta yawo da shari'ar

Alkali Ahmed Mohammed aka fara kawowa wannan shari’a, daga baya aka maida karar gaban Inyang Ekwo, a karshe kuma ta zo hannun Obiora Egwuatu.

A hukuncin da Mai shari’a Obiora Egwuatu ya zartar a ranar Litinin, ya umarci DSS ta biya Naira miliyan 1 ga Omoyele Sowore saboda an tauye masa hakkinsa.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Hukuncin kotu ya zo daya

Wannan hukunci ya zo daidai da wanda kotu tayi a kan gwamnatin tarayya saboda tarwatsa zanga-zangar #RevolutionNow da Sowore suka jagoranta a 2019.

Olukoya Ogungbeje shi ne lauyan da ya kai karar gwamnatin tarayya zuwa gaban Maureen Onyetenu.

Da take zartar da hukunci a kotun tarayya da ke garin Legas, Onyetenu ta ce abin da aka yi bai halatta ba, ya ci karo da dokar kasa, ya sabawa damukaradiyya.

Jaridar ta ce haka aka yi a Disamban 2021 inda Anwuli Chiekere ta bukaci DSS ta biya Sowore kudi har N2m saboda an karbe masa wayoyinsa ba da dalili ba.

Shari'ar Abba Kyari

Ku na da labari cewa bisa dukkan alamu mummunan labari zai je wa Abba Kyari wanda ya yi bikin cika shekara 47 a tsare a hannun hukumar NDLEA kwanaki.

Ministan shari'a ya bada dama NDLEA ta karbe gine-gine, kudi, dukiyar da ke banki, kadarori abubuwan hawa, hannun jari da duk wani abu mai daraja na su Kyari.

Kara karanta wannan

2023: Ina Neman Goyon Bayan Ku Don Cika Burin Rayuwa Ta, Tinubu Ga Sanatocin APC

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng