Da dumi-dumi: Sabon gwamna ya yi sabbin nade-nade kwanaki bayan rantsar dashi
- Kwanaki kadan bayan rantsar da shi a matsayin gwamnan jihar Anambra na shida, Farfesa Chukwuma Soludo ya yi sabbin nade-nade a mukamai guda uku
- Daga cikinsu, Gwamna Soludo ya nada Richard Nwora Madiebo, a matsayin shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Anambra
- Tuni dai gwamnan jihar na Anambra a ranar rantsar da shi ya bayyana nada wasu muhimman mukamai guda uku
Awka, jihar Anambra – Farfesa Chukwuma Soludo, sabon gwamnan jihar Anambra, ya bayyana nadin karin mukamai uku, inji rahoton jaridar The Punch.
A cewar sanarwar a birnin Awka, a ranar Litinin, 21 ga watan Maris, sabbin mutane uku da aka nada sune:
- Mista Ernest Ezeajuyi a matsayin shugaban ma’aikatan Gwamnan
- Mista Richard Nwora Madiebo, shugaban hukumar tattara kudaden shiga na jihar Anambra
- AVM Ben Chiobi (Rtd.), mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin tsaro
Legit.ng ta lura cewa, wannan ya zama jimillar nade-nade shida da gwamnan ya yi tun hawansa, inda ya yi uku a ranar rantsar da shi a matsayin gwamna a ranar Alhamis, 17 ga watan Maris.
A ranar Alhamis ne gwamnan ya bayyana nadin Farfesa Solo Osita Chukwulobelu, sakataren gwamnatin jihar, Dr Sir Chukwudi Okoli, Akanta Janar, Mista Chinedu Nwoye, mataimakin shugaban ma’aikata/shugaban kula da harkokin jihar.
Ya kuma yi alkawarin aika jerin sunayen kwamishinoninsa zuwa majalisar jihar a mako mai zuwa, kamar yadda sanarwar da kafar yada labarai ta Anambra ta wallafa.
Ku saki Obiano komu mamaye Hedkwatarku tsirara, Matan Anambra sun ja kunnen EFCC
A wani labarin, wata kungiyar mata a jihar Anambra, ta yi barazanar mamaye hedkwatar hukumar EFCC dake Abuja ba tare da kaya a jikin su ba.
Punch ta rahoto cewa kungiyar mai suna, 'Anambra-North Women Empowerment Movement' ta yi barazanar ne matukar hukumar yaki da cin hanci ta ki sako tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano.
Kungiyar ta yi Allah wadai da wani Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka ga Obiano na shan ruwa a Ofishin EFCC da yake tsare.
Asali: Legit.ng