Buhari ya aikawa Gwamna, Minista da Hadiminsa gayyata, ya na nemansu yau a ofishinsa

Buhari ya aikawa Gwamna, Minista da Hadiminsa gayyata, ya na nemansu yau a ofishinsa

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci ganin wasu manyan gwamnati a fadar Aso Villa
  • Muhammadu Buhari zai gana da Gwamna Hope Uzodinma a kan rikicin da ya barke a jihar Imo
  • Shugaban Najeriyar zai kuma yi wani zaman da Ministan harkar wuta da hadiminsa, Doyin Salami

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aika sammaci ga gwamnan jihar Imo, Ministan harkar wutar lantarki da mai ba shi shawara kan tattali.

Garba Shehu ya fitar da sanarwa a ranar Litinin, 21 ga watan Maris 2022 yana cewa Mai girma Muhammadu Buhari ya bukaci ganin wadannan mutane.

Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce Muhammadu Buhari zai yi zama da Gwamna Hope Uzodinma, Injiniya Abubakar Aliyu da Farfesa Doyin Salami.

Kara karanta wannan

Tambuwal: Lamarin Buhari da Najeriya tamkar auren dole ne tsakanin namiji da mace

Kamar yadda sanarwar wanda ta fito a Facebook ta nuna, shugaban Najeriyan zai yi wannan zama da Shugabannin ne a mabanbantan lokuta a yau da rana.

Hakan ya biyo bayan matsalar rashin wutan da ake samu a halin yanzu da kuma zaman dar-dar da ake yi a jihar Imo, da kuma halin tattalin arzikin Najeriya.

Rashin tsaro a Imo

Shehu ya ce a baya, shugaba Buhari ya yi Allah-wadai da tashin-tashinan da ake yi a jihar Imo inda wasu tsageru suka tada hatsaniya a kudu maso gabas.

Buhari
Shugaba Buhari a taron FEC Hoto: @MBuhari
Asali: Twitter

An ruguza gine-gine, sannan an yi wa ‘yan sanda barna a mahaifar shugaban kungiyar Ohaneze Ndigbo mai kare hakkin mutanen Ibo, watau George Obiozor.

Matsalar wutar lantarki

Bayan haka, Muhammadu Buhari ya koka a game da rashin wutan da ake samu a mafi yawan wurare, har kuma ya sha alwashin za a shawo kan lamarin.

Kara karanta wannan

Inyamuri nike son ya zama shugaban kasa a 2023, Obasanjo

Malam Buhari Sallau ya fitar da jawabin hadimin shugaban kasar a shafinsa na Facebook dazu.

Haduwa da Doyin Salami

Wannan zai kasance yana cikin zaman da Buhari ya yi da mai ba gwamnatinsa shawara a kan harkar tattalin arziki, Farfesa Doyin Salami wanda ya nada a 2022.

Doyin Salami ya dare wannan kujera bayan an yi kusan shekaru bakwai babu wanda yake ba Buhari shawara kai-tsaye a kan duk abin da ya shafi tattalin arziki.

Ina aka kai gangunan mai?

A makon jiya ne aka ji cewa a shekarar 2019, NNPC ta fitar da ganguna sama da miliyan 100 na danyen man fetur a Najeriya, amma babu labarin inda aka kai kudinsu.

Duk wadannan sun faru ne a shekarar 2019, a lokacin da Muhammadu Buhari yake shugaban kasa. Mai girma Buhari ke rike da kujerar Ministan harkar mai tun 2015.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng