Yanzu-yanzu: Awa 10 da sauka daga mulki, EFCC ta damke Willie Obiano yana shirin guduwa Amurka
- Tarkon hukumar EFCC ya kama tsohon gwamna Willie Obiano yayinda yake kokarin guduwa Amurka
- Da safiyar nan Willie Obiano ya mika mulki ga Farfesa Charles Chukwuma Soludo sannan ya shilla jihar Legas
- Hukumar EFCC tuni ta sanar da jami'an tsaro su hana Obiano fita daga Najeriya dan ya sauka daga mulki
Hukumar hana almundana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC a dare Alhamis ya damke tsohon gwamnan jihar Anambra, Willie Obiano, a tashar jirgin Murtala Muhammad dale Lagos.
EFCC ta damke Obiano ne misalin karfe 8:30 na dare.
An ce yana kokarin guduwa Houston a kasar Amurka ne bayan mika mulki ga sabon Gwamna Charles Soludo.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A watan Nuwamba, hukumar EFCC ta sanya sunan Willie Obiano cikin wadanda take dako.
EFCC ta bukaci hukumar shiga da fice ta sanar da ita duk lokacin da Gwamnan ke kokarin fita daga kasar ta sama ko ta kasa.
Ku saki Obiano ko mu mamaye Hedkwatarku tsirara, Matan Anambra sun ja kunnen EFCC
Wata ƙungiyar mata a jihar Anambra, ta yi barazanar mamaye hedkwatar hukumar EFCC dake Abuja ba tare da kaya a jikin su ba.
Punch ta rahoto cewa ƙungiyar mai suna, 'Anambra-North Women Empowerment Movement' ta yi barazanar ne matukar hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙi sako tsohon gwamnan Anambra, Willie Obiano.
Ƙungiyar ta yi Allah wadai da wani Bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta, wanda aka ga Obiano na shan ruwa a Ofishin EFCC da yake tsare.
A wata sanarwa da kungiyar ta raba wa yan jarida a Awka, ranar Litinin, shugabar ƙungiyar Uju Ifunanya Edochie, ta zargi EFCC da nuna tozarci.
Asali: Legit.ng