Labari cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari

Labari cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi takakkiya daga Dubai, kasar UAE zuwa Landan don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 16 ga MAris 2022.

Gwamnan wanda shine Shugaban kwamitin rikon kwarya ya tafi Landan daga Dubai inda yake jinya don ganin Buhari bisa tsigeshi da akayi daga kujerarsa shugaban jam'iyyar.

Buni yace ta ajiye wasikar wakilta gwamnan Neja, Abu Bello, ya taya rike jam'iyyan kan ya dawo amma Bello ya ce shi bai ga wasikar ba.

Wannan ziyara da Gwamnan ya kai ya biyo bayan rikicin dake gudana cikin jam'iyyar ta APC yayinda ake shirin taron gangamin jam'iyyar ranar 26 ga Maris.

Labarin cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari
Labarin cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Jam'iyyar APC ta fasa taron majalisar zartaswar gobe

Labarin cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari
Labarin cikin Hotuna: Mai Mala Buni yayi takakkiya zuwa Landan don ganin Shugaba Buhari
Asali: Twitter

Shugaba Buhari ya yi magana rikicin shugabancin APC da ranar babban taro

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya yi tsokaci kan rikicin shugabanci da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa a jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

A wata sanarwa da kakakinsa, Malam Garba Shehu, ya fitar a Facebook, shugaba Buhari ya gargaɗi jagororin APC da su guji kiran suna da cin dudduniyar junansu.

Shugaban ƙasa ya kuma jaddada cewa babban ganganmin jam'iyyar APC na ƙasa na nan daram ranar da aka tsara 26 ga watan Maris 2022.

Haka nan Buhari ya roki mambobin APC da su kawar da duk wani saɓani dake tsakanin su, kuma su haɗa kai matukar suna son jam'iyyar ta cigaba da samun nasara a dukkan matakai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng