Da ɗuminsa: An damƙe ɗan saƙo ya ɓoye jinjiri a akwatin saƙo a Legas, bidiyo ya bayyana

Da ɗuminsa: An damƙe ɗan saƙo ya ɓoye jinjiri a akwatin saƙo a Legas, bidiyo ya bayyana

  • Fusatattun jama'a sun lakadawa wani mai kai sako mugun duka a jihar Legas inda suka ja shi a kasa har ofishin 'yan sanda
  • An kama matashin mai babur ne da yaro dan goye a cikin akwatin kai sako a yankin Sangotedo da ke jihar Legas
  • Har a halin yanzu ba a san yadda aka yi yaron ya shiga akwatin ba duk da jama'a sun dinga ihun cewa yaron da ake nema ne aka gani

Legas - Jama'a sun cafke dan kai sako a jihar Legas yayin da aka kama shi da jinjiri a cikin akwatin kai sako.

Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin ya faru ne a yankin Sangotedo da ke jihar Legas yayin da fusatattuna jama'a suka far wa matukin babur din kai sakon.

Kara karanta wannan

A kan bashin N2.7m da ta ke bin sa, magidanci ya nada wa matarsa mai juna biyu dukan mutuwa

Da ɗuminsa: An damƙe ɗan saƙo ya ɓoye jinjiri a akwatin saƙo a Legas
Da ɗuminsa: An damƙe ɗan saƙo ya ɓoye jinjiri a akwatin saƙo a Legas
Asali: Original

Wani bidiyon lamarin da ya faru an wallafa a Twitter inda aka bayyana ana nadar dan sakon yayin da ake jan shi a kasa har zuwa ofishin 'yan sanda.

Daya daga cikin mutanen da ke wurin an ji yana cewa: "Wannan shi ne jinjirin da aka sace."

Har a halin yanzu 'yan sanda ba su yi magana kan aukuwar lamarin da ya janyo cece-kuce duba da yawaitar miyagun laifuka a jihar.

A yayin rubuta wannan rahoton, ba a gano yadda aka yi jaririn ya shiga akwatin ba.

Sanannen abu ne yadda yankin Sangotedo da ya hada da Ajah, Abijo da Lekki suka zama fitattun yankunan a Legas da aka fi samun masu laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: