Hisbah ta yi ram da zuka-zukan 'yan mata a gidan saurayi suna shan wiwi da miyagun kwayoyi
- Hukumar Hisbah a jihar Kebbi ta yi ram da wasu 'yan mata masu kananan shekaru a gidan saurayinsu suna tsaka da shan wiwi da kwayoyi
- Hukumar ta ce ba wannan bane karon farko da ta kama farida Malami da Sadiya Isah suna aikata wannan laifukan ba
- Fitaccen malamin addinin Islama, Malam Tukur Kola, ya bukaci iyaye da su dinga sa ido kan 'ya'yansu tare da kiyaye abokan huldarsu
Birnin Kebbi, Kebbi - A ranar Alhamis ma'aikantan hukumar Hisbah ta jihar Kebbi sun kama wasu yara masu kananun shekaru, Farida Malami da Sadiya Isah, dukkan su daga Birnin Kebbi, suna ta'ammuli da miyagun kwayoyi a anguwar Rafin Atiku na Birnin Kebbi.
Kamar yadda kwamandan rundunar Hisbah, Suleiman Muhammad wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin ya bayyana yadda aka kama yaran mata guda biyun a gidan saurayin su dumu-dumu suna shan wiwi, maganin tari da sauran miyagun kwayoyin masu matukar illa ga al'umma.
Ya kara da cewa, wannan shi ne karo na biyu da kwanan nan aka sake kama wadannan dai yaran da suka ki nadama.
A hukuncin shi, Alkali mai shari'a, Abubakar Lambe Augie ya ce, an mika su ga hukumar NDLEA don gyaran hali da taimakon matar gwamnan jihar Kebbi, Dr Zainab Shinkafi Bagudu, wacce ta biya duk kudin da aka kashe a gidan gyaran hali.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ta bada tallafi, gami da kokarin Barista Maryam Kaoje, wacce ta taimaka wajen tabbatar hukumar NDLEA ta tsare su gami da mika su gidan gyaran hali, Vanguard ta ruwaito.
Wani fitaccen malamin addinin musulunci, Malam Tukur Kola, wanda yayi wa yaran wa'azi, ya bukaci iyayen yaran da su dunga lura da shige da ficen yaran su da kuma kawayen da suke hulda dasu.
NDLEA ta kwace kwayoyin Tramadol 649,300 a filin jirgin sama na Legas
A wani labari na daban, jami'an hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) sun kama a kalla kwayoyin Tramadol masu nauyin 225mg guda 649,300 da Euro809,850 da sauran miyagun kwayoyi da aka shigo dasu daga Pakistan, Australia da Italiya a titin jirgin Murtala Muhammad (MMIA) na Ikeja dake jihar Legas.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce, a ranar Lahadi a Abuja, jami'an hukumar sun kara kama sauran miyagun kwayoyin da aka shigo dasu daga Turai, America da Canada a wannan filin jirgin.
Kamar yadda ya bayyana, a kamfanin kula da sufirin jiragen sama na Skyway, ma'aikatan hukumar sun kwace kwayoyin Tramadol na 225mg guda 549,300 masu nauyin kilo 460.95 wanda aka shigo dasu daga Pakistan ta Addis Ababa ta jirgin Ethiopia a ranar 16 ga watan Fabrairu, tare da kama wani wanda ake zargi, Nwadu Ekene Christian.
Asali: Legit.ng