Hajj da Umrah: Bukatar rigakafin Korona da wasu dokoki 6 da Gwamnatin Saudiyya ta soke
Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da soke dukkan dokokin kariya daga cutar COVID-19 da aka sanyawa shiga Masallacin haramin Makkah da na Madinatul Munawarrah.
Tun shekarar 2020 da Korona ta bulla, ma'aikatar lafiya Saudiyya ta kafa jerin dokokin da ya wajaba abi don kare rayukan mutane daga cutar.
Hakan yasa a shekaru biyu jere, ba'a bari maniyyata daga kasashen waje su gudanar da aikin Hajji ba.
A ranar Lahadi, gwamnatin kasar ta soke dukkan dokokin kamar yadda Haramain Sharifain ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga jerin dokokin da Saudiyya ta soke:
1. An soke dokar bada tazara tsakanin Masallata a Masallacin Makkah da Madina amma a sanya takunkumin fuska
2. Babu bukatar mutum yayi rigakafin Korona ko ya gabata da hujjar cewa bai da cutar kafin shiga kasar Saudiyya daga waje
3. Soke dokar duba lafiyar mutum kafin a bari a shiga Masallacin Makkah da Madina
4. Babu bukatar rijistar bayanan rigakafi ga maniyyatan Umrah da Hajji daga kasashen waje
5. Soke dokar killace yan kasar waje da suka shiga Saudiyya a Otal na yan kwanaki
6. An amince yara (ko daga wani kasa) su fara shiga Masallacin Haram da Masallacin Madina ko sunyi rigakafin Korona ko basu yi ba
7. Maniyyata daga kasashen duniya zasu samu damar Umrah ko basu nuna hujjar rigakafi ba
Saudiyya ta dage wasu dokokin Korona yayin da Ramadana ke karatowa
Kasar Saudiyya ta ce ta dauke mafi yawan takunkumin Korona da suka hada da ba da tazara yayin sallah da kebe masu shigowan da suka yi rigakafin Korona, matakan da za su iya saukakawa masu shiga kasar domin ibada.
Shawarar ta ce hakan zai shafi wurare daban-daban na taro a kasar, ciki har da masallatai, in ji majiyar ma'aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya.
Sai dai, za a bukaci mutane suke sanya takunkumin fuska a wuraren da suke rufe, bisa ga shawarar, wacce ta fara aiki ranar Asabar.
Asali: Legit.ng