Muhimman lamurra 6 da ya dace a sani game da yakin Rasha da Ukraine bayan mako 2 da farawa

Muhimman lamurra 6 da ya dace a sani game da yakin Rasha da Ukraine bayan mako 2 da farawa

A yayin da rikicin Rasha da Ukraine ya cika kwanaki 15, sojojin Rasha sun mamaye a kalla manyan birane hudu na kasar yayin da aka shirya birnin Kyiv domin ko ta kwana.

Har a yanzu babban birnin Ukraine na karkashin ikon kasa amma akwai yuwuwar Rasha ta kwace shi domin yadda take ta hararo shi, The punch ta ruwaito.

Ga takaitattun al'amuran da ke faruwa ta kowanne bangare a yakin Rashan da Ukraine.

Muhimman lamurran 6 da ya dace a sani game da yakin Rasha da Ukraine bayan mako 2 da farawa
Muhimman lamurran 6 da ya dace a sani game da yakin Rasha da Ukraine bayan mako 2 da farawa. Hoto daga punchng.com
Asali: UGC

Gabas

Har yanzu birnin Kharkive na hannun Ukraine duk da tsananta ruwan bama-bamai da Rasha ta yi a birnin kamar yadda majiyoyi daga yammaci suka ce, kuma a halin yanzu garin a zagaye yake.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dakarun Rasha sun kara matsa lamba ta yankunan Donetsk da Lugansk duk da har yanzu ba a san yadda suka ratsa ba, The punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Duk mai sha'awar shiga yakin Ukraine kuma bai da $1k na biza, ya zo Arewa ya nuna kwarewarsa a yaki

Birnin Sumy a arewa maso gabashin Ukraine a halin yanzu zagaye yake da dakarun rasha. Amma fararen hula dubu biyar sun samu damar tserewa a ranar Talata a cikin motoci sittin.

Kyiv da arewaci

Kyiv har yanzu tana karkashin ikon Ukraine duk da ruwan wuta da ake musu, duk da masu lura daga yammaci sun gano cewa akwai daruruwan ababen hawa a wajen birnin.

Ma'aikatar tsaron Birtaniya ta ce ana rikici a arewa maso yammacin Kyiv amma dakarun Rasha sun kasa samun nasara.

Kudanci

Rasha ta zagaye birnin Mariupol kuma yunkurin kwashe farar hula dubu dari biyu daga birnin ya gagara.

Kwace birnin zai bai wa dakarun Rasha damar shiga har arewacin Ukraine kusa da peninsula of Crimea.

Yammaci da tsakiya

Har a halin yanzu yammacin Ukraine ba ta san ana wannan artabun ba. Babban birnin Lviv ta zama madaddalar 'yan diflomasiyyan kasashen waje da 'yan jarida da kuma 'yan kasar Ukraine da ke neman mafaka ko kokarin barin kasar.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: An Sanar Da Ranar Da Rasha Da Ukraine Za Su Yi Zaman Tattauna Tsagaita Wuta

Wadanda lamarin ya ritsa da su

A ranar Talata, majalisar dinkin duniya ta ce an rasa fararen hula 474 a Ukraine kuma akwai kananan yara 29 a ciki duk da har yanzu ba a san takamaiman yawansu ba.

Ukraine da majiyoyin yammaci sun yi ikirarin cewa yawan jama'ar da suka mutu a Moscow ya fi yawan yadda Rasha ke sanarwa.

Ukraine ta ce sama da sojojin Rasha dubu goma sha biyu aka kashe, duk da US ta yi kiyasin cewa an kashe mutum dubu biyu zuwa dubu hudu ne daga Rasha.

'Yan gudun hijira

Wasu mutum miliyan 2.16 ne suka tsere gudun hijira daga Ukraine tun bayan kutse da Rasha tayi wanda sama da rabinsu suka shige Poland, kamar yadda hukumar gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ta bayyana.

An fara kwasan fararen hula daga biranen Irpin da Sumy

Hukumomi a kasar Ukraine sun bayyana cewa an fara kwashe fararen hula daga birnin Irpin da Sumy bayan Rasha ta tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Mamayar Rasha: Mutane miliyan 1 sun yi gudun hijira a Ukraine cikin mako 1, UNHCR

Ammam har yanzu ba'a san halin da fararen hulan Mariupol ke ciki ba saboda dakarun Rasha sun ragrgaza hanyoyin fita. Fadar shugaban Rasha ta bayyana cewa ta tsagaita wuta don a kwashe faaren hula daga birnin Ukraine, Kyiv, Chenihiv da Kharkiv.

Amma ba'a sani ko an fara kwashewan a halin yanzu ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng