An tasa keyar dan adawan Ganduje, Dan Bilki Kwamanda, gidan gyaran hali
- Mai sharhi kan lamuran siyasa a jihar Kano ya shiga jerin wadanda Gwamna Ganduje ya kai kotu
- Kotun majistare bayan sauraron karar ta bada umurnin ajiye Danbilki a gidan gyara hali kafin ya samu beli
- Wannan ya biyo bayan daure tsohon kwamishanan Ganduje, Dan Sarauniya Muazu Magaji
Kano - Wata kotun majistare dake zamanta a unguwar Nomanland a cikin garin Kano ta tasa keyar wani dan adawar Gwamna Abdullahi Ganduje, Abdulmajid Danbilki Kwamanda.
An gurfanar da shi a kotu ne kan zargin batanci da sharri wa gwamna Ganduje, rahoton DailyTrust.
Rahotanni sun nuna cewa Danbilki ya zargi Ganduje da laifin bada cin hanci ga Mai Mala Buni da mambobin kwamitinsa don tabbatar da cewa Abdullahi Abbas, ya zama Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano.
Alkalin kotun, Aminu Magashi, a ranar Talata ya bada umurnin tasa keyar Kwamanda zuwa gidan yari bayan watsi da bukatar belin da lauyansa yayi.
Danbilki dai ya musanta laifin da ake zarginsa da shi.
Alkalin kuwa ya dage karan zuwa ranar 15 ga Maris, 2022.
Dan Bilki Kwamanda ya shahara da caccakan Gwamna Ganduje a gidan rediyo.
Shine mutum na biyu a baya-bayan nan da gwamnan zai maka a kotu.
Muazu Magaji bai dandara ba, ya dawo Facebook daga barin kurkuku
An shafe kusan makonni biyu ba tare da an ji duriyar Mu’az Magaji wanda aka fi sani da ‘Dansarauniya a dandalin sada zumunta na Facebook ba.
Dalilin kuwa shi ne ana ta faman shari’a da Injiniya Mu’az Magaji, wanda har ta kai an tsare shi.
A yammacin Laraba, 16 ga watan Fubrairu 2022 kewan da masoya suke yi wa Mu’az Magaji ya zo karshe, aka ga ya fito shafinsa a Facebook, ya yi magana.
Da kimanin karfe 8:20 na dare ne Jagoran tafiyar Win-Win ko Kano sabuwa a siyasar Kano watau ‘Dansarauniya ya yi maganar farko a shafinsa tun a Junairu.
‘Dan siyasar ya shafe kwanaki 20 rabonsa da Facebook, abin da ba a saba gani daga wurinsa ba. A ranar 27 ga watan Junairu ya yi maganar karshe a shafinsa.
Asali: Legit.ng