Miyagu sun shigo gida, sun babbaka Mai Unguwa har lahira yayin da aka fita sallar asuba
- Ana zargin wasu ‘yan iskan gari da laifin babbaka Basarake har lahira a yankin kudancin Najeriya
- Da asuba aka ji uwargida ta na ihu, wuta ta kona Baalen kasar Olowe Gbagura, Akin Muheedeen
- Matan Oba Akin Muheedeen sun tabbatar da cewa an iske wuta tana cin shi bayan an kashe shi da safe
Ogun - Mai martaba Baalen kasar Olowe Gbagura a garin Abeokuta, jihar Ogun watau Akin Muheedeen ya gamu da ajalinsa. Punch ta fitar da wannan rahoto.
Ana zargin wasu mutane ne suka cinnawa Cif Akin Muheedeen wuta, hakan ya yi sanadiyyar ajalinsa.
Jaridar ta ce mutanen gari su na zargin abin ya faru ne a lokacin da Mai martaba ya shirya zai je sallar asuba, a sa’ilin ne wasu suka auka masa, su ka babbaka shi.
Mazauna karamar hukumar Abeokuta ta Arewa, sun shaidawa Daily Trust cewa wadannan miyagun mutane sun shiga gidan mai martaban da suka fasa taga.
Bayan sun hallaka Oba Muheedeen, sai suka cinna masa wuta, inda ya babbake kafin gari ya waye.
Rikicin fili kafin ya mutu
Mai martaba Baale ya samu sabani da wasu daga cikin talakawansa kwanan nan a game da batun fili. Daily Trust ta ce ba a dade sosai da yin wannan rikicin ba.
A dalilin wannan rigima ne aka kama Mai martaban, aka tsare shi saboda hannunsa a rigimar filin.
An shirya cewa Mai garin zai bayyana a kotu a ranar 15 ga watan Maris 2022, sai kwatsam aka ji labarin mutuwarsa. Yanzu haka an bar iyali da jama’a da makokinsa.
Yadda abin ya faru - Matansa
Wata daga cikin matar Mai garin mai suna Silifat, ta tabbatar da aukuwar wannan lamari. Silifat ta ce ta dawo daga sallar asuba ne sai ta hangi wuta na ci a gidansu.
Iyabode wanda a dakin ta ne Mai martaban ya kwana a daren, ta ce ya tashi zai je kama ruwa domin ya yi sallar asuba da kimanin karfe 6:00, sai ta ji bai dawo ba.
Kwatsam sai ta ji uwargidar tana ihun cewa wuta ya kama gida. Nan take sai ta iske Baale yana ci da wuta, Iyabode ta ce ba su san wa ya yi wannan danyen aiki ba.
Kisan Oba Ayinde Odetola
Kwanaki an ji yadda wasu ‘yan iskan gari da ba a san su wanene ba suka shiga karamar hukumar Ewekoro, su ka kashe Sarkinsu, Mai martaba Oba Ayinde Odetola.
Rikici a kan wanda zai mulki kasar Alagado tsakanin mutanen Ake da Owu ne ya jawo wannan ta’adi. An kona Oba Ayinde Odetola ne tare da wasu na-kusa da shi.
Asali: Legit.ng