Borno: Dakarun sojin Najeriya sun yi artabu da mayakan ISWAP, an yi musayar wuta

Borno: Dakarun sojin Najeriya sun yi artabu da mayakan ISWAP, an yi musayar wuta

  • Dakarun sojin Najeriya sun yi artabu da wasu miyagu da ake zargin 'yan ta'addan Boko Haram ne a garin Damboa da ke Borno
  • Kamar yadda majiyoyi suka tabbatar, sun kwashe kusan mintuna talatin suna musayar wutar tsakaninsu da 'yan ta'addan
  • An tabbatar da cewa zakakuran dakarun sojin Najeriyan sun samu nasarar dakile farmakin yayin da mayakan ta'addanci suka tsere

Borno - A yammacin Litinin, rundunar sojin jihar Borno tayi musayar wuta da wasu da ake zargin mayakan ISWAP ne, a karamar hukumar Damboa ta jihar Borno.

Kamar yadda majiyoyin suka bayyana, musayar wutar ya dau kimanin minti 30, Daily Trust ta ruwaito.

Borno: Dakarun sojin Najeriya sun yi artabu da mayakan ISWAP, an yi musayar wuta
Borno: Dakarun sojin Najeriya sun yi artabu da mayakan ISWAP, an yi musayar wuta. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

An tattaro yadda Mayakan ISWAP suka auka wa anguwan Biu ta babban titi, kafin dakarun su yi nasarar dakile harin.

"Dakarun sun yi nasarar dakile harin a Damboa. Musayar wutar ta kai kimanin minti 25, kafin su tsere ta hanyoyi daban-daban," a cewar majiyar.

Kara karanta wannan

Nasrun Minallah: Sojoji sun yi kazamin artabu da yan ta'adda, sun aika 17 ga Allah a Borno

Daily Trust ta ruwaito cewa, mayakan ISWAP sun dade suna cin Karen sy ba babbaka a sansani daban-daban na arewa maso gabas.

ISWAP na horar da masu kunar bakin wake domin kai wa hukumomin tsaro hari, DSS

A wani labari na daban, bayan wani binciken sirri da hukumar tsaron farin kaya tayi, ta ce ta gano yadda mayakan ISWAP ke horar da masu kunar bakin wake yadda za su kai hari ga jami'an tsaro da yankunan kasar nan.

Haka zalika, DSS ta bayyana yadda wasu daga cikin ISGS dake yankin tafkin Cadi, wadanda suka yi hijira zuwa Mali, bayan takura musu da sojojin da rasha tayi haya suka yi, inda suka shigo kasar Najeriya don karfafa ayyukan yan ta'addan ISWAP, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Mummunar gobara ta lamushe kadarorin N18m a Mariri

Shugaban SDES na jihohin arewa maso gabas, Babagana Bulama, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Maiduguri, babban birnin jihar Borno. Hukumar ta hada taron, domin ta duba kalubalen dake tunkaro yankin, TheCable ta ruwaito.

Bulama, wanda kuma shi ne daraktan DSS a jihar Adamawa, ya bayyana yadda shiyyar arewa maso gabas ke cigaba da fuskantar kalubalen tsaro iri-iri.

"Manya daga cikin matsalar tsaron da shiyyar nan ke fuskanta shi ne yadda Boko Haram da ISWAP suke cin karen su ba babbaka a shiyyar.
"Duk da ire-iren hare-hare da 'yan ta'addan ke kaiwa ya ragu cikin kwanakin nan, lokacin da jami'an tsaro suke dakile ta'addanci, bayanan sirri sun nuna yadda ISWAP ke horar da masu kunar bakin wake da shirin kai farmaki ga jami'an tsaro da yankunan da suke yawan kai hari," yace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: