Hotunan Farfesa Pantami yayin gwajin motar da aka kera a Najeriya mai amfani da wutar lantarki
- Farfesa Ali Isa Ibrahim Pantami ya yi gwajin mota mai amfani da wutar lantarki da aka kera a Najeriya a kwanakin nan
- Ministan ya shiga motar da kansa, inda aka ganshi tare da daraktan hukumar kula da kera motoci na Najeriya suna gwajin
- Wannan dai ita ce kusan mota ta farko da Najeriya ta kera mai amfani da wutar lantarki, tare da hadin gwiwa da kamfanin Huandai
FCT, Abuja - Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani ya yi gwajin wata mota mai amfani da wutar lantarki da aka kera a Najeriya.
Ya yi gwajin motar ne jim kadan bayan da hukumar kula da kera motoci ta kasa (NADDC) ta kawo masa ziyarar aiki a ofishinsa da ke Abuja.
Tagawar ta NADDC tana karkashin jagorancin Darakta Janar na hukumar ne Mista Jelani Aliyu, MFR.
Wata sanarwa ta ma'aikatar sadarwar Najeriya ta fitar ta nuna hotunan lokacin Farfesa Pantami ke cikin mota yayin da yake gwajin motar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kalli hotunan da ministan ya yada ta shafinsa na Facebook:
Tambuwal ya gwada mota kirar Najeriya mai aiki da wutan lantarki
Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya amshi motar Kona mai aiki da Wutar Lantarki wacce Hukumar Kula da kera motoci da cigaban motoci ta kasa (NADDC) tare da hadin gwiwar kamfanin Stallion suka bude kwanan nan.
Ku tuna cewa a ranar 5 ga watan Fabrairu, NADDC, a karkashin jagorancin Darakta-Janar na ta, Jelani Aliyu, ta gabatar da motar mai aiki da lantarki ta farko da aka kera a cikin gida mai suna Hyundai Kona, a Abuja.
Motar an sanya mata farashin Naira miliyan 24 ga kowane daya, tare da ba da garantin batir da kira na tsawon na shekara 5, 100% aiki da lantarki, ba amfani da mai za kuma a iya cajinta a gida da wajen aiki, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng