Nasrun Minallah: Sojojin Najeriya sun tura yan ta'adda 17 lahira a Borno
- Gwarazan sojojin Najeriya na Operation Hadin Kai, sun tura yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 17 su haɗu da Allah a jihar Borno
- Kwamandan OPHK, Manjo Musa, ya ce yan ta'addan sun gamu da luguden wutan soji ta sama da kasa yayin da suka kai farmaki sansanin Walada
- A jawabinsa, ya ce dakarun sun damƙe yan ta'addan uku da ransu, kuma sun kwato motoci da makamai
Borno - Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarun Operation Hadin Kai (OPHK) sun halaka yan ta'addan Boko Haram/ISWAP 17 a Damasak, karamar hukumar Mobbar, jihar Borno.
Jaridar Guardian ta rahoto cewa Garin Damasak, hedkwatar karamar hukumar Mubbar, na kusa da tafkin Yobe da kuma Tafkin Komadugu Gana River, ya haɗa iyaka da jahar Neja.
Kwamandan OPHK na arewa maso gabashin Najeriya, Manjo Janar, Christopher Musa, shi ne ya sanar da nasarar sojojin yayin hira da hukumar dillancin labarai ta kasa (NAN) ranar Litinin a Maiduguri.
Kwamandan ya ce dakarun sojojin ba su tsaya iya nan ba, sun damƙe yan ta'addan guda uku da ran su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Manjo Musa ya yi bayanin cewa dakarun sun kwato motoci da wasu makamai daga hannun yan ta'addan yayin farmakin da suka kai ranar Laradi.
Daily Nigerian ta rahoto Kwamandan sojin ya ce:
"Sojoji sun yi gumurzu da adadi mai yawa na yan ta'adda yayin da suka yi kokarin kai hari sansanin sojoji dake kusa da Walada, a garin Damasak da karfe 2:00 na dare."
Yadda lamarin ya faru
Musa ya ƙara da cewa yan ta'addan sun kwashi kashin su a hannun jajirtattun sojojin, waɗan da suka jure artabu da su ba kakkautawa, bisa tilas yan ta'addan suka tsere.
Bugu da kari Manjo Janar Musa ya bayyana cewa sojojin sun samu taimako daga dakarun sojin sama, suka rutsa yan ta'addan ta sama da ƙasa.
Yayin da yake kalaman yabo ga gwarazan sojin, Musa ya kuma kara musu caji kan su cigaba da jajircewa wajen kawo karshen ayyukan yan ta'adda baki ɗaya.
A wani labarin na daban kuma An tsinci gawar mai haɗa wa Mataimakin shugaban ƙasa takalmi a daki a Abuja
Omale Ojima mai haɗa Takalma a babban birnin tarayya Abuja , ya mutu daga kwanciya bacci a ɗakinsa dake Kubwa.
Wani mazaunin yankin ya ce lokacinsa ne ya yi, domin ya kwanta lafiya lau, da safiyar Lahadi aka tsinci gawarsa a daki.
Asali: Legit.ng