Da duminsa: Jami'an tsaro sun mamaye sakateriyar APC ta kasa dake Abuja
- Jami'an tsaro sun zagaye farfajiyar sakateriyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta kasa dake Abuja
- Rahotanni sun bayyana cewa shugaba Buhari ya tsige Buni daga mukaminsa na shugabancin jam'iyyar, lamarin da sakataren jam'iyyar ya musanta
- An ga 'yan sanda sun hana shige da fice daga sakateriyar inda wani yace sun je dakile tada hankula ne
FCT, Abuja - Jami'an tsaro sun mamaye sakateriyar jam'iyyar All Progressives Congress (APC) dake Abuja.
Akwai rahotannin da ke bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tunbuke gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, daga mukamin shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar.
An tattaro cewa, gwamnan jihar Niger, Sani Bello ne zai karba ragamar jam'iyyar, Daily Trust ta ruwaito.
Amma a yayin martani kan rahoton, sakataren kwamitin rikon kwaryan, Sanata John James Akpanudoedehe, ya ce babu batun sauyin shugabanci a jam'iyyar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Hankulanmu sun kai zuwa ga wani rahoto da aka dauka nauyi wanda ke bayyana sauyin shugabanci na kwamitin rikon kwarya da shirya zaben shugabannin jam'iyyar All Progressives Congress (APC)."
"Rahoton babu gaskiya a cikinsa kuma ku yi watsi da shi. Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) jam'iyya ce da ke da dokoki. Ba kowanne kafa bane ke iya sanar da sauyin shugabanni ba a kafafen yada labarai.
A halin yanzu, dukkan hanyoyin da ke kaiwa sakateriyar a Wuse 2 a rufe suke, hakan ya hana ababen hawa kaiwa da kawowa.
Daily Trust ta gano cewa, an hana shige da fice kai tsaye ga mambobi da ma'aikatan sakateriyar.
Wani dan sanda ya sanar da cewa: "Mun bayyana ne domin hana barkewar tarzoma."
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng