Badakalar kwayoyi: Bayan kwanaki 20 a tsare, za a shiga kotu da Abba Kyari da mutum 6
- An jima ne ake tunanin DCP Abba Kyari zai bayyana gaban Alkali Emeka Nwite a babban kotu a Abuja
- Za a fara shari’a da Abba Kyari da wasu abokan aikinsa; ACP Sunday J. Ubia, da ASP Bawa James
- Sauran wadanda ake zargi da harkar kwayoyi su ne: Insp. Simon Agirigba da wani Insp. John Nuhu
Abuja - Jaridar Sun ta kawo rahoto a ranar Litinin cewa an jima ake sa ran a maka DCP Abba Kyari da wasu mutane shida a gaban babban kotun tarayya.
Rahoton ya ce za a gurfanar da jami’in ‘dan sandan da sauran mutane shida da ake zargi da hannu a harkar kwayoyi a kotun da ke zama a babban birnin Abuja.
Hukumar NDLEA za ta yi shari’a da su DPC Kyari a kan zargin aikata laifuffuka takwas da suka shafi safarar kwayoyi a gaban Alkali Mai shari’a Emeka Nwite.
Sauran wadanda za su kare kansu a wannan shari’a mai lamba FHC/ABJ/57/2022 sun hada da jami’an tsaro; Ubia, Bawa James, Simon Agirigba da John Nuhu.
Ragowar su ne mutanen da ake zargin an kama da kwayoyi a filin jirgin Akanu Ibiam na Enugu; Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne.
NDLEA ta je kotu
Jaridar Vanguard ta ce darektan harkokin shari’a na hukumar NDLEA, Joseph Sunday ya kai kara kotu, yana zargin wadannan mutane da aikata manyan laifuffuka.
Sunday ya ce Kyari da sauran ‘yan sandan hudu su na da hannu wajen kutun-kutun da cinikin kilo 17.55 na hodar iblis. Wannan babban laifi ne a dokar kasa.
Su kuma Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus Ezenwanne za su amsa laifin shigo da kilo 21.35 na hodar iblis cikin Najeriya ta babban filin jirgin.
Makonni 3 a garkame
Tun ranar 14 ga watan Fubrairun 2022 ne Kyari da sauran wadanda ake zargi su ke tsare, ana yi masu tambayoyi a kan neman bada rashawar daloli da suka yi.
Ana tuhumar jami’an ‘yan sandan da yunkurin biyan wani ma’aikacin NDLEA kudi har $61, 400 domin ya saki wasu tulin hodar iblis da ya karbe a jihar Enugu.
A baya an kai kara gaban Alkali Inyang Ekwo domin a fito da Kyari. Amma Alkalin ya ce NDLEA ta samu umarnin cigaba da tsare su a wajen wata babbar kotu.
Karin matsaloli
A baya ku na da labarin cewa binciken ‘yan sanda ya bankado yadda Ramon Abass watau Hushpuppi da mutanensa suka aika N235, 120, 000 ga kanin Kyari.
Binciken da aka yi ya kuma nuna DCP Abba Kyari wanda aka dakatar daga aiki ya tura N44m zuwa asusun wannan kanin na sa a lokuta dabam-dabam ta banki.
Asali: Legit.ng