Sifeto Janar IGP Alkali ya amince Mata yan sanda su fara sanya Hijabi

Sifeto Janar IGP Alkali ya amince Mata yan sanda su fara sanya Hijabi

  • Hukumar yan sandan Najeriya ta saki jerin sabbin kayan da ya hallata mata jami'ai su rika sanyawa
  • Daga cikin hukumar ta amince daga yanzu mata jami'ai su rika sanya dan kunne maras jela
  • Hakazalika an amincewa mata sanya dan kwali mai kama da Hijabi don rufe gashinsu

Birnin tarayya Abuja - Sifeto Janar na yan sanda, IGP Baba Alkali, ya amince jami'an yan sanda mata su fara sanya dan kwali mai kama da Hijabi kan kayan sarki.

Wannan ya bayyana a hotunan sanarwar da hukumar tayi kwanakin nan.

An bayyana sabon tsarin ne a ganawar IGP na manyan jami'an yan sanda ranar 3 ga Maris 2022.

IG Baba ya bayyana cewa hukumar yan sanda na da jami'ai a dukkan kananan hukumomin jihar mai mutane masu mabanbantan addini da al'ada.

Kara karanta wannan

Hisbah ta yi ram da zuka-zukan 'yan mata 2 suna shan wiwi da miyagun kwayoyi

Saboda haka akwai bukatar girmama addinan mutane don kwantar musu da hankali wajen gudanar da ayyukansu.

IG ya bayyana cewa tuni kasashe irin Canaga, Amurka, Sweden, Turkiyya, Birtaniya da Australiya na sanya irinw wannan kaya.

Kalli hoton:

Sifeto Janar IGP Alkali ya amince Mata yan sanda su fara sanya Hijabi
Sifeto Janar IGP Alkali ya amince Mata yan sanda su fara sanya Hijabi
Asali: Facebook

Ji nake kamar nayi kuka idan dan sanda ya aikata laifi, IGP Alkali Baba

Sifeto Janar na yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, a ranar Talata ya bayyana bacin ransa bisa yadda ake aikata laifuka a fadin kasa.

IGP, wanda da alamun yana magana ne kan lamarin jami'an dan sandan da aka dakatar Abba Kyari, ya bayyana hakan yayin ziyarar kwana guda da ya kai hedkwatar yan sandan Abuja, rahoton TheNation.

Yace:

"Muyi abinda ya dace a lokacin da ya dace. Ji nake kamar nayi kuka idan aka kama yan sanda da aikata laifuka."

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng