An gano sabon salon da Boko Haram suka dauka tun da dakarun Sojoji sun ci karfinsu
- Alkaluman da Global Terrorism Index suka fitar ya nuna ana neman cin galaba a kan Boko Haram
- Sojojin Najeriya da na kasashen waje sun tasa ‘Yan Boko Haram a gaba, sun yi masu illa a kasar nan
- A dalilin haka, ‘Yan ta’addan sun koma kai hari a kasar Kamaru da ke makwabtaka da Najeriya
Nigeria - Wani rahoton Global Terrorism Index (GTI) na 2022 ya bayyana cewa hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram ya yi matukar raguwa a Najeriya.
Jaridar Premium Times ta ce yayin da Najeriya ta ke jin dadin wannan labari, kasashen da ke makwabtaka da ita su na fuskantar karin barazana a yau.
A shekarar 2021, Najeriya ta sauko daga ta uku a jerin kasashen da suke fama da matsalar ta’addanci, a halin yanzu kasar ce ta shida a fadin Duniya.
Afghanistan ce ta farko yayin da Iraki da Somoliya suke biya da ita. Sauran kasashen da suka sha gaban Najeriya a shekarar nan su ne Burkina Faso da Siriya.
Hare-haren B/Haram sun yi sauki
Alkaluma sun nuna ta’adin sojojin Boko Haram da suka yi fiye da shekaru 10 su na ta’addanci musamman a yankin Arewa maso gabashin Najeriya ya ragu.
Rahoton da GTI ta fitar a ranar Laraba ya tabbatar da cewa mutane 69 kadai aka tabbatar da cewa ‘Yan Boko Haram sun kashe a 2021, adadin ya yi kasa da 77%.
Jaridar ta ce a shekaru goma da suka wuce, adadin wadanda ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram suka yi sanadiyyar mutuwarsu bai taba yin kasa irin haka ba.
Rundunar sojojin Najeriya da na kasashen ketare su na ragargazar mayakan Boko Haram da ISWAP, hakan ya rage masu tasiri a ‘yan shekarun bayan nan.
An komawa makwabta
A sakamakon luguden da jami’an tsaro suke ta yi masu a Najeriya, sojojin na Boko Haram sun koma kai hari a wasu kasashen makwabta kamarsu Kamaru.
A 2021, Boko Haram ta kai hari sau 37 a kasar Kamaru, inda ta kashe mutane akalla 58. Shekara ta biyu kenan a jere da aka fi addabar Kamaru a kan Najeriya.
Murkushe Boko Haram da ake yi yana kuma da alaka da mutuwar shugabanta watau Abubakar Shekau. Sannan ‘yan ta’addan su na fama da sabani na gida.
Kasashe masu karfin nukiliya
Mun kawo maku wani rahoto na jerin kasashe masu karfin nukiliya inda ku ka ji cewa Kasashe 8 sun sanar da Duniya cewa su na dauke da makaman kare dangi.
Kasashen Rasha da Amurka su ke da 90% na makaman nukiliyan Duniya. Sannan Kasar Israila ta mallaki nukiliya a boye, shekaru fiye da 50 kenan ta na boye da su.
Asali: Legit.ng