'Yan Najeriya da ke kasar Ukraine za su fara isowa kasar nan a ranar Juma'a
- Kashi na farko na 'yan Najeriya mazauna kasar Ukraine za su iso gida a ranar Juma'a sakamakon yakin da ya barke da kasar
- Jiragen kamfanonin Max Air da Air Peace sun dira a kasar Poland da Romania tun ranar Alhamis domin kwaso 'yan Najeriyan
- A kalla 'yan Najeriya dubu biyar za a kwaso daga kasashen Poland, Hungary, Slovakia da Romania
Wasu 'yan Najeriya da suka tsere daga Ukraine yayin da kasar Rasha ke tsaka da luguden wuta a kasar, za su iso Najeriya a ranar Juma'a.
Jiragen kamfanonin jiragen sama na Najeriya, Max Air da Air Peace sun isa kasashen Romania da Poland a ranar Alhamis domin kwaso su.
Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya aike jirginsa zuwa Warsaw, babban birnin kasar Poland yayin da Max Air ta aike jirginta kasar Romania.
Kusan 'yan Najeriya dubu biyar ne suka cancanci a dawo dasu gida, Channels TV ta ruwaito.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Tashin jirgin da ya je kasar Poland ya samu tsaiko ne a ranar Alhamis sakamakon tsaikon da aka samu wurin shirya fasinjojin da za su dawo gida, jami'i daga ma'aikatar harkokin waje, Bolaji Akinremi yace.
An sauya lokacin tashin jirgin daga kasar Poland zuwa safiyar Juma'a, Channels TV ta ruwaito.
A daya bangaren, jirgin Romania zai sauka filin sauka da tashin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a safiyar Juma'a.
A ranar Laraba, gwamnatin tarayya ta amince da fitar da $8.5 miliyan domin kwaso 'yan kasarta.
Kamar yadda karamin ministan harkokin waje, Zubairu Dada yace, za a kwaso 'yan Najeriya daga kasashen Poland, Hungary, Slovakia da Romania.
Mun shirya: Najeriya za ta fara gina tashar makamashin nukiliya, ta hada kai da Rasha, da wasu kasashe
A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa yanzu haka an bude yunkurin gwamnati na gina tashar makamashin nukiliya mai karfin megawatt 4000.
A cewar rahoton Nairametrics, Dokta Yau Idris, Darakta Janar na Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Najeriya (NNRA) ne ya bayyana hakan a yayin wani taron koli na makamashi na kasa da kasa na Najeriya (NIES) da ke gudana a Abuja.
Idan har aka yi nasara aka kammala aikin, Idris ya yi ikirarin cewa masana'antar za ta kasance babbar tashar samar da wutar lantarki a kasar.
Asali: Legit.ng