Sanusi II: Abu 1 da ya sa Jonathan da Ganduje suka tsige ni daga CBN da sarautar Kano

Sanusi II: Abu 1 da ya sa Jonathan da Ganduje suka tsige ni daga CBN da sarautar Kano

  • Malam Muhammadu Sanusi II ya yi bayanin abin da ya kai shi ga rasa kujerar gwamnan CBN da sarauta
  • Tsohon Sarkin Kano ya ce fadawa masu mulki gaskiya ne dalilin da ya sa aka sauke shi daga matsayinsa
  • A jawabinsa, tsohon gwamnan na CBN ya dauko abin da ya faru tsakanin mahaifinsa da Janar Murtala

Abuja - The Guardian ta rahoto Muhammadu Sanusi II yana cewa karfin halinsa na fadawa masu mulki gaskiya ne ya rasa mukaman da ya rike a kasar nan.

Tsohon Sarkin ya yi wannan bayani ne a wajen rufe wani taro da aka shirya domin koyar da shugabanci. An yi wannan taron ne a birnin tarayya Abuja.

Sanusi II ya koka da halin ma’aikatan da ake da su a yau, ya ce maimakon su rika bin ka’idar aiki domin kawo cigaba, mafi yawa sun sa abin Duniya a gaba.

Kara karanta wannan

Minista ya yi wa daliban jami’a albishir, ASUU ta kusa janye yajin-aikin da ta shiga

“Ma’aikacin gwamnati yana yi wa kasar Najeriya aiki ne ba wani shugaban kasa, gwamna ko wani Minista ba.”
“An manta da wannan a kasar nan. Shiyasa bangarorin shari’a, kiwon lafiya, noman wuta da ilmi duk ba su aiki.”
“Ina ba ku shawarar ku yi murabus idan har ku na aiki, kuma ba za ku iya taimakawa mutanen da ya dace ba.”
Sanusi II
Sanusi Lamido Sanusi Hoto: Patrick T. Fallon/Bloomberg Daga: Getty Images
Asali: Getty Images

“Idan ba ku kawo tsare-tsare da za su amfani jama’a ba, ku sani cewa gazawarku za ta shafi ‘ya ‘yanku wata rana.”

Rasa matsayinsa a Najeriya

Sarkin da aka tunbuke daga sarauta ya ce dalilin sauke shi daga matsayin gwamnan babban banki shi ne fadin gaskiya da kokarin yin abin da yake daidai.

A yau ana samun ma’aikatan gwamnati su na satar dukiyar da za ayi wa al’umma aiki. A ganinsa hakan ya jawo ake fama da ‘yan bindiga da kuma Boko Haram.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Idan na shiga Aso Villa, kowane yaro zai yi karatu kyauta inji Sanatan APC

Aminu Sanusi v Murtala Mohammed

Daily Trust ta ce Sanusi II ya bada labarin abin da ya auku tsakanin mahaifinsa a lokacin yana ma’aikatar harkokin waje a gwamnatin su Murtala Mohammed.

Sanusi II ya ce Aminu Sanusi ya ki bada sunayen ma’aikatan da za a kora daga aiki a 1975, ya tsaya tsayin daka, a karshe babu wanda aka kora a ma’aikatarsa.

A shekarar bara, an ji Mai martaba Muhammadu Sanusi II, ya yi magana a game da tunbuke shi da Gwamna Dr. Abdullahi Ganduje ya yi daga sarautar gidan dabo.

Khalifan na darikar Tijjaniya a Najeriya, Malam Muhammadu Sanusi II ya ce da gan-gan da ya hakura da sarautar Kano bayan kusan shekara shida ya na sarauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng