Najeriya na gab da rugujewa gaba daya, Farfesa Attahiru Jega
- Malamin makaranta kuma tsohon baturen zaben Najeriya ya bayyana cewa kasar nan na bukatar ceto na gaggawa
- Jega wanda yace a ra'ayinsa, Najeriya na gab da rugujewa gaba daya saboda irin kidahuman shugabanninta dake jagoranci
- Attahiru Jega ya yi kira ga masu kishin kasar nan su kawo mata dauki na gaggawa
Abuja - Tsohon Shugaban hukumar shirya zaben kasa watau INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya bayyana cewa Najeriya na gab da rugujewa saboda ganganci da mulkin makafin da ake mata.
Jega ya bayyana hakan ne ranar Laraba a taron da kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta shirya a birnin tarayya Abuja, rahoton Vanguard.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa, dubi ga yadda abubuwa ke gudana a kasar nan yanzu, da alamun zaben 2023 kadai zai iya bayyana halin da ranar goben kasar nan zata shiga.
A cewarsa,
"Ko da kasar bata gama rugujewa ba gaba daya, tana hanyar rugujewa saboda gangancin da masu mulki ke yi da kuma tukin makahon da ake wa kasar. Zaben 2023 zai bayyana halin da kasar ne zata shiga gobe."
"Saboda haka, akwai bukatar masu kishin kasa su hada karfi da karfe wajen ceto kasar nan daga rugujewa zuwa kasa mai shugabannin kwarai, cigaban kwarai, da tsaro ga 'yayanta."
Hukumar INEC ta sanar da ranar zaben shugaban kasa na 2023
Hukumar shirya zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta sanar da ranar da za'a gudanar da zaben shugaban kasa, yan majalisa da gwamnoni na shekarar 2023.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya sanar da hakan a hira da manema labarai ranar Asabar a birnin tarayya Abuja.
A cewarsa, za'a gudanar da zaben Shugaban kasa da na majalisar dokokin tarayya ranar Asabar, 25 ga watan Febrairu, 2023.
Yayinda na gwamnoni da majalisar dokokin jiha zasu gudana ranar Asabar, 11 ga Maris, 2023.
Asali: Legit.ng