Gwamnatin PDP ta maka EFCC a kotu saboda an nemi jin ina aka kai Biliyoyin kudin jiha

Gwamnatin PDP ta maka EFCC a kotu saboda an nemi jin ina aka kai Biliyoyin kudin jiha

  • Gwamnatin jihar Oyo za tayi shari’a da EFCC a kotun tarayya saboda hukumar ta na kokarin bincikenta
  • Jami’an EFCC sun taso gwamnatin Oyo a gaba tun 2021, su na neman jin inda aka kai wasu kudin jihar
  • Wannan ya sa Gwamnati ta dauki hayar Lauyoyi, ta na kalubalantar aikin EFCC a tsarin mulkin kasa

Oyo - Alkalin babban kotun tarayya da ke Ibadan, jihar Oyo, U. N. Agomoh ya fara yin hukunci a kan gwamnatin jihar Oyo da hukumar EFCC ta kasa.

Jaridar Tribune ta kawo rahoto cewa Mai shari’a U. N. Agomoh ya bukaci EFCC da gwamnatin Oyo su dakata daga daukar mataki yayin da suke kotu.

Hakan na zuwa ne bayan gwamnatin jihar Oyo ta shigar da karar EFCC a gaban kotun da ke Ibadan a dalilin tsare babban akanta na jihar, Gafar Bello.

Kara karanta wannan

2023: Dattawan Arewa Sunyi Taro, Sun Yanke Shawarar Goyon Bayan Igbo Ya Maye Gurbin Buhari

A ranar Juma’a ne gwamnatin ta je kotu, ta na korafin cewa hukumar EFCC ta addabe ta tun Agustan 2021 game da yadda ta batar da wasu kudinta.

EFCC tana neman karin bayani a kan yadda gwamnatin Oyo ta kashe kudin tsaro da abin da ke cikin asusun tattara haraji da adana kudin in-ta-kwana.

Gwamnati Seyi Makine
Seyi Makine tare da Buhari Hoto: www.herald.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

EFCC ta saba doka?

Gwamnatin ta na ganin EFCC ba ta da hurumin da za ta binciki yadda aka yi da wadannan kudi domin sashe na 176 na dokar kasa ce ta ba gwamna dama.

Lauyoyin gwamnati sun fadawa kotu cewa kundin tsarin mulkin da ya damkawa Mai girma gwamna wuka da nama ya sha gaban dokar da ta kafa EFCC.

Independent ta ce a ranar Talata Alkali ya saurari shari’ar mai lamba ta FHC/IB/23/22. Ana zargin N9bn sun yi kafa daga kudin kananan hukumomin jihar Oyo.

Kara karanta wannan

ASUU ta magantu kan sabuwar N1trn da ake yadawa tana bukata daga FG

Har ila yau, lauyoyin da suka tsayawa gwamnatin Oyo sun ce sassa na 80 da na 88 ba su ba kowa damar bincike a kan wadannan kudi ba sai majalisar tarayya.

Gwamnatin ta ce a sashe na 120 zuwa 128 na tsarin mulki, wanda aka ba alhakin binciken gwamna kan zargin facaka da kudin jiha su ne majalisar dokoki.

Buhari ya kunyata 'yan adawa

Kun ji yadda Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ba marada kunya bayan an ce ba zai taba amincewa ya sanya hannunsa a kan kudurin dokar zaben ba.

A karshen shekarar 2021 aka ji Buba Galadima yana cewa a fille masa kai, idan aka sa hannu a kan sabon kudirin zaben, kuma daga baya Buhari ya sa hannunsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng