NCC ta bankado manhajar ‘yan damfara a ‘Android’ da ke satar sirrin dukiyar mutane
- Hukumar NCC ta ce akwai wata barauniyar manhaja da ta shiga kasashen Duniya, tana yin barna
- Wata sanarwa daga sashen Computer Security Incident Response Team ta ankarar da masu Android
- An kirkiro wata manhaja da ake kira Xenomorph da ke iya samun bayanan bankuna daga Android
Abuja - Hukumar nan ta NCC ta bayyana cewa ta gano wata muguwar manhaja wanda ke yin kutse domin satar bayanan sirrin mutane a wayoyin zamani.
Daily Trust ta ce sashen Computer Security Incident Response Team (CSIRT) na hukumar ta NCC ne ta bayyana wannan a wata sanarwa da ta fitar a makon jiya.
Kamar yadda NCC-CSIRT suka bayyana, ana zargin wannan manhaja mai suna “Xenomorph” ta na harin manyan kamfanoni 56 a wasu kasashen da ke Turai.
Barauniyar manhajar ta shiga manhajojin bankuna 28 a Sifen, 12 a kasar Italiya, 9 a Belgium, da 7 a Portugal da kuma wasu manhajojin kudin Cryptocurrency.
Hadarin Xenomorph
Hukumar ta ce wannan manhaja ta “Xenomorph” ta na da matukar hadari da damar yi wa mutane kutse.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jaridar Blueprint ta ce manufar “Xenomorph” ita ce satar bayanan sirrin shiga manhajojin bankuna a wayoyin Android ta hanyar amfani da sakonni na SMS.
An yi amfani da Fast Cleaner
An cusa Xenomorph ne ta karkashin wata manhaja da ake saukewa a rumbun Play Store. Ana kiran wannan manhajar da aka fake da ita ne da ‘Fast Cleaner’
Mai magana da yawun bakin NCC na kasa, Ikechukwu Adinde ya ankarar da al’ummar Najeriya.
Ikechukwu Adinde ya ce ana amfani da Fast Cleaner ne domin rage cunkoso a wayoyin Android da kuma inganta kyawun batir, a haka aka cusa Xenomorph Trojan.
Xenomorph Trojan zai iya ganin sakonnin da suka shigo waya, hakan zai sa ya samu bayanan bankin mutum ko da kuwa ana amfani da fasahar tsaro na 2-Factor.
Duk da Google ta dauke Fast Cleaner, an yi wa mutane illa domin an sauke shi fiye da sau 50, 000.
Harin 'yan ta'adda a Kaduna?
A ranar Litinin ne aka ji Gwamnatin jihar Kaduna ta ankarar da jama’a a kan yiwuwar ‘yan ta’adda na shuka bama-bamai a makarantu da otel da hanyoyi.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar da jawabi yana gargadin mutanen jihar Kaduna bayan wani bam ya tashi a unguwar Kabala.
Asali: Legit.ng