Allah ya yiwa mahaifiyar Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar AlFurqan rasuwa

Allah ya yiwa mahaifiyar Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar AlFurqan rasuwa

  • Babban Malamin Addinin Musulunci kuma Injiniya, Dr Bashi Aliyu Umar ya yi rashin mahaifiyarsa
  • Za'ayi jana'izar Hajiya a fadar mai marata Sarkin Kano bayan Sallar Azahar
  • Manyan Maluma sun aika sakonnin ta'azziyarsu ga babban Malamin

Labarin da ke shigo mana da duminsa na nuna cewa Allah ya yiwa mahaifiyar Limamin Masallacin AlFurqan dake jihar Kano, Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar rasuwa.

Daliban Babban Malamin addinin Islaman sun bayyana hakan ne a shafin Malamin na Facebook.

Sun sanar da cewa za’ayi mata Sallar Jana’iza misalin karfe uku na rana a gidan Sarkin Kano.

Jawabin yace:

Bisa sallamawa ga ƙaddarawar Allah ta’ala muke sanar da rasuwar mahaifiyar Babban malaminmu Dr. Bashir Aliyu Umar.
In Sha Allah Jinaza karfe 3 na Yamma Kofar Kudu Gidan Sarkin Kano.

Kara karanta wannan

Muhammad Hassan Nasiha: Abubuwa 5 Da Ya Kamata Ka Sani Game Da Sabon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara

Muna roƙon Allah ya Bata firdausi madaukakiya

Dr Bashir Aliyu Umar AlFurqan rasuwa
Allah ya yiwa mahaifiyar Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar AlFurqan rasuwa Hoto: Dr Bashir
Asali: Facebook

Sheikh musa yusuf Asadus-Sunnah yace:

"Ina miqa sakon ta'aziyyata ga Babban Malamin mu Sheikh Dr Bashir Aliyu Umar Babban Limamin Masallacin Alfurqan abisa Rasuwar Mahaifiyarsa Hajiya Khadijah.
Allah ya ji kanta da Rahama ya sa ta huta ya bawa iyalai da 'yan Uwa da Abokan arzuki hakuri da Juriyyar Rashin da aka yi da duk musulman da su ka mutu Allah ya gafarta musu in tamu ta zo ya sa mu cika da kyau da imani."

Dr Ibrahim Disina:

Allah yayi rasuwa wa mahaifiyar Malaminmu (Haj Khadiza) rasuwa, Mahaifiyace ga Dr Imam Bashir Aliyu umar Yau, za ayi mata sallar janaza da kafe 3pma kofar Kudu a birnin Kano in sha'allah, Allah ya jikanta ta da Rahama ameen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Tags: