Yanzu-yanzu: Shugaba Buhari zai tafi birnin Landan ganin Likita na tsawon makonni 2
1 - tsawon mintuna
- Kamar yadda ya saba shekara-shekara, Shugaba Buhari zai sake shillawa birnin Landan ganin Likita
- Da farko zai fara zuwa kasar Kenya don halartan wani taro daga nan kuma ya tafi Landan inda zai kwashe makonni 2
- Tun bayan ciwon kunnen da yace yana fama da shi, har yanzu yan Najeriya basu san abinda Buhari ke zuwa Landan ba
Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari zai tafi Landan, kasar Birtaniya, don ganin Likitocinsa na tsawon makonni biyu bayan halartan taron majalisar dinkin duniya da za'ayi a Kenya.
Mai magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adesina, ya tabbatar da hakan a jawabin da ya saki ranar Talata.
Ya ce:
"Shugaba Buhari zai tashi daga Abuja yau Talata 1 ga Maris don halartan murnar cika shirin majalisar dinkin duniya na yanayi shekaru 50 (UNEP@50), da aka shirya yi ranar 3-4 ga Maris, 2022, a Nairobi, Kenya, sakamakon gayyatar da takwararsa na Kenya, Uhuru Knyatta yayi masa."
Adesina yace Shugaba Buhari zai samu rakiyar Ministan harkokin waje, Geoffrey Onyeama; Karamar ministar yanay, Sharon Ikeazor; NSA Manjo Janar Babagana Monguno; DG na NIA, Ambasada Rufai Abubakar, da Shugabar hukumar yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa.
Ya kara da cewa Buhari zai gabatar da jawabi a taron.
Asali: Legit.ng
Tags: