Bam ya tashi cikin dare a Kaduna – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan abin da ya auku

Bam ya tashi cikin dare a Kaduna – ‘Yan Sanda sun yi karin haske kan abin da ya auku

  • Jami’an tsaro sun tabbatar da fashewar wani bam a yankin Kabala West da ke cikin garin Kaduna
  • Jami’an ‘yan sanda sun fitar da sanarwa ta musamman, sun tabbatar da aukuwar wannan lamari
  • Mohammed Jalige ya yi jawabi a madadin ‘yan sanda, ya yi alwashin cewa za su gudanar da bincike

Kaduna - Wani makami ya tashi a yankin Kabala, a karamar hukumar Kaduna ta kudu a jihar Kaduna a ranar Lahadi, 27 ga watan Fubrairu 2022.

Hukumar dillacin labarai na kasa watau NAN ta fitar da wannnan rahoto, NAN ta bayyana cewa ana zargin irim bam dinnan na IED ne ya tashi a jiya.

Rundunar ‘yan sanda na reshen jihar Kaduna, ta yi magana a game da batun, ta tabbatar da cewa lamarin ya auku ne cikin dare a karshen makon jiya.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa Da Sarki a Jihar Arewa

Mai magana da yawun bakin ‘yan sanda na jihar Kaduna, Mohammed Jalige ya shaidawa manema labarai babu shakka wani bam ya tashi a Kabala.

Babu wanda aka rasa

Da yake bayani a safiyar Litinin, Mohammed Jalige ya bayyana cewa an taki sa’a domin babu wanda ya samu rauni a ginin da wannan bam ya tashi.

Bam ya tashi a coci
Wnai lokacin da bam ya tashi a Kaduna Hoto: allafrica.com
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Nigerian ta fitar da rahoto, bam din ya tashi ne da kimanin karfe 9:45 na dare.

Rahoton ya nuna jami’an tsaron ba su yi kasa a gwiwa ba, domin an aika da dakaru na musamman.

“Tuni an aika da dakarun da ke cire bam zuwa yankin da abin ya faru domin su yi bincike a kan kasar da aka samu.” - Mohammed Jalige.

A jawabin da ya fitar, Mohammed Jalige ya yi alkawarin cewa ‘yan sanda za su yi bincike domin gano abin da ya faru, da nufin a dauki matakin da ya dace.

Kara karanta wannan

Bayan watanni 6, an gurfanar da wadanda ake zargi da hallaka yaron Sanata a gaban kotu

Shekarun baya, jihar Kaduna ta na cikin inda aka yi fama da matsalar rashin tsaro har ta kai ana harba bam. Zuwa yanzu dai abubuwan sun yi sauki sosai.

Yakin Rasha

A halin yanzu da Rasha ta ke yakar kasar Ukraine, an ji cewa Shugaba Volodymyr Zelensky ya bayyana adadin sojojin kasan da aka rasa daga soma rikicin.

Volodymyr Zelensky ya yi jawabi a shafinsa na Facebook, ya ce Rasha ta kashe masu sojoji sama da 130. Baya ga haka akwai wasu sojoji 300 da suka samu rauni.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng