Yaki: Amurka, Birtaniya, kasashe 25 zasu taimakawa Ukraine da makamai

Yaki: Amurka, Birtaniya, kasashe 25 zasu taimakawa Ukraine da makamai

Kwanan uku da fara yakin dake gudana tsakanin Rasha da Ukraniya, kasashen duniya ashirin da bakwai (27) sun yi alkawarin aikewa jami'an Ukraine makamai, magunguna dss, Sky News ta ruwaito.

Wadannnan kasashe sun hada da Amurka, Birtaniya, da sauran kasashen nahiyar Turai.

Rahoton yace:

"Kayan tallafin sun hada da makamai, na'urar kariya daga igwa, na'urar kawar a harbin sama da kuma magunguna."

Wannan ya biyo bayan ganawar bada tallafin kayan yaki da Sakataren tsaron Birtaniya, Ben Wallace, ya shirya da yammacin Juma'a inda kasashe 25 da suka hallara suka yi alkawari.

Kasashe biyun da basu samun daman halarta ba sun yi nasu alkawarin ranar Asabar.

Gabanin wannan sanarwa, Shugaban kasar Amurka ya rattafa hannu kan sabuwar umurnin baiwa kasar Ukraine tallafin kayan yakin $600m.

Kara karanta wannan

Shin na taba fadi zaben fidda gwani ne?, ina da tabbaci: Atiku ya yi alfahari

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng