Ta wani dalili zamu jinkirta jirgin da ya fara tafiya saboda mutum 1, Air Peace ya yi raddi

Ta wani dalili zamu jinkirta jirgin da ya fara tafiya saboda mutum 1, Air Peace ya yi raddi

  • Kamfanin jirgin Air Peace ya fadi nasa jawabin kan zargin da ake masa na wulankanta mai martaba Sarkin Kano
  • Isa Sanusi Bayero wanda aka fi sani da Isa Pilot ne ya aika wasika ga NCAA a kan abin da ya kira cin mutunci da aka yi wa Sarkin Kano
  • Air Peace yace sabanin abinda ake yadawa na cewa kamfanin ya ci mutuncin Sarkin, kare mutuncin Sarkin akayi

Jihar Legas - Kamfanin jirgin sama na Air Peace, ya bayyana cewa ko kadan bai ci mutuncin mai martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ba.

Shugabar harkokin ayyyukan kamfanin, Toyin Olajide, a jawabin da ta saki ta bayyana cewa karya Isa Bayero ya sharara saboda kamfanin Air Peace na ganin girman Sarkin Kano matuka.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wani ma'aikacin jami'a ya mutu a cikin ruwan shakatawa a Hotel

A cewarta, sabanin abinda ake yadawa na cewa kamfanin ya ci mutuncin Sarkin, kare mutuncin Sarkin akayi.

Ta wani dalili zamu jinkirta jirgin da ya fara tafiya saboda mutum 1, Air Peace ya yi raddi
Ta wani dalili zamu jinkirta jirgin da ya fara tafiya saboda mutum 1, Air Peace ya yi raddi
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Olajide tace:

"Sabanin raina Mai martaba Sarkin Kano da aka ce anyi, AirPeace ya yi komai don kare mutuncin Sarkin ta hanyar kin sauraron abinda (Isa) Bayero yace muyi."
"Da mun yarda mun jinkirta jirgin da ya shirya tashi na tsawon awa guda sannan Sarkin Kano ya shigo, mutane zasu tada jijiyoyin wuya a kafafen yada labarai kan kamfanin da Sarkin. Shi yasa muke baiwa Bayero hakuri amma yaki yarda."
"Ta wani dalili Isa Bayero ke son kamfanin Air Peace ya hana jirgin da ya cika tashi bayan an kulle kofa kuma ya fara tafiya yayinda Mai martaba Sarki da tawagarsa, ciki har da Isa Bayero, na cikin sashen jiragen waje na tashar jirign Murtala Muhammad Legas bayan dawowa daga Banjul?"

Kara karanta wannan

Yadda Air Peace su ka ‘ci mutuncin’ Sarki Aminu Ado Bayero da tawagarsa a filin jirgi

Air Peace ya ‘ci mutuncin’ Sarki Aminu Ado Bayero da tawagarsa a filin jirgi, Fadar Kano

Wani daga cikin ‘yanuwan Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya rubuta takardar korafi zuwa ga hukumar NCAA ta tarayya.

Daily Trust ta ce Isa Sanusi Bayero wanda aka fi sani da Isa Pilot ne ya aika wasika ga NCAA a kan abin da ya kira cin mutunci da aka yi wa Sarkin Kano.

Isa Sanusi Bayero ya zargi kamfanin jirgin Air Peace da cin zarafin Sarki da mutanen kasar Kano.

A wannan takarda ta korafi, Alhaji Isa Pilot ya koka a kan yadda jirgin saman ya bata masu lokaci daga Banjul zuwa Legas, inda suka bata sama da sa’a guda.

Bayan haka, ‘danuwan Sarkin ya fadawa hukumar NCAA cewa kamfanin jirgin saman sun yi sanadiyyar da Mai martaba ya rasa jirgin da ya tashi zuwa Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng