Yadda Air Peace su ka ‘ci mutuncin’ Sarki Aminu Ado Bayero da tawagarsa a filin jirgi

Yadda Air Peace su ka ‘ci mutuncin’ Sarki Aminu Ado Bayero da tawagarsa a filin jirgi

  • Kwanaki an samu takaddama tsakanin tawagar Aminu Ado Bayero da kamfanin jirgin Air Peace
  • Kamfanin sun jawo Mai martaba ya bata lokaci a filin jirgi a Banjul har ta kai bai dawo Kano ba
  • Ana korafin cewa da aka nemi alfarma wajen shugaban Air Peace, ya wulakanta Aminu Ado Bayero

FCT, Abuja - Wani daga cikin ‘yanuwan Mai martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya rubuta takardar korafi zuwa ga hukumar NCAA ta tarayya.

Daily Trust ta ce Isa Sanusi Bayero wanda aka fi sani da Isa Pilot ne ya aika wasika ga NCAA a kan abin da ya kira cin mutunci da aka yi wa Sarkin Kano.

Isa Sanusi Bayero ya zargi kamfanin jirgin Air Peace da cin zarafin Sarki da mutanen kasar Kano.

Kara karanta wannan

Rasha vs Ukraine: Ku Rufa Mana Asiri, Ku Ja Bakinku Ku Yi Shiru, 'Yan Najeriya Sun Shawarci FG

A wannan takarda ta korafi, Alhaji Isa Pilot ya koka a kan yadda jirgin saman ya bata masu lokaci daga Banjul zuwa Legas, inda suka bata sama da sa’a guda.

Bayan haka, ‘danuwan Sarkin ya fadawa hukumar NCAA cewa kamfanin jirgin saman sun yi sanadiyyar da Mai martaba ya rasa jirgin da ya tashi zuwa Kano.

Kamar yadda Platinum Post ta kawo rahoto, Sarki Aminu Ado Bayero da ‘yan tawagarsa sun iso tashar jirgin na Legas ne minti 30 bayan jirgin Kano ya tashi.

Aminu Ado Bayero
Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero Hoto: aminu.adobayero.1
Asali: Facebook

Zargin wulakancin Allen Onyeama

Isa Pilot ya ce ya kira shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyeama, ya fada masa halin da ake ciki, ya nemi alfarmar a daga tashin jirgin da zai je Kano.

An saba yi irin haka, a bata lokaci wajen tashin jirgin sama domin a girmama wani mai mukami ko martaba. Amma Allen Onyeama ya ce sam ba zai yi ba.

Kara karanta wannan

Alkali ya bada umarni hukumar EFCC ta karbe gidan tsohon Gwamnan APC a Abuja

“Nan take ya fada mani cewa ba zai yi wannan ba. Na dauki wannan a matsayin cin mutunci da kuma rashin daraja Mai martaba da duka mutanen Kano.”

- Isa Pilot

Pilot ya ce dole Sarki da mutanensa suka kama otel su na jiran wani jirgin ya zo. A haka kuma sai da aka bukaci su biya karin kudi saboda sun ki hawa jirginsu.

A 2019 ne aka ji cewa shugaba Muhammadu Buhari ya nada Kyaftin Musa Nuhu a matsayin sabon DG na hukumar kula da zirga-zirgan jiragen Sama a Kasa.

Shugaban NCAA na kasa, Kyaftin Musa Nuhu ya samu wannan wasika, amma bai ce uffan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng