Buhari ya nada sabon shugaba a NCAA

Buhari ya nada sabon shugaba a NCAA

Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Kyaftin Musa Nuhu a matsayin sabon Direkta-Janar na Hukumar Kula da Zirga-Zirgan jiragen Sama ta Kasa, NCAA.

Mista Nuhu zai maye gurbin Kyafyin Mukhtar Usman a matsayin shugaban hukumar kamar yadda sanarwar da Jami'in Hulda da Al'umma na hukumar, James Odaudu ya fitar a Abuja a ranar Laraba.

Mista Odaudu ya ce, "Kafin nadin Nuhu, shi ne wakilin Najeriya na dindindin a kungiyar kasa da kasa da sufurin jiragen sama, kuma matukin jirgin sama ne kana kwararre kan fanoni daban-daban a bangaren aikin jiragen sama."

DUBA WANNAN: Da duminsa: FG ta canja wa ma'aikatar sadarwa suna

Sabon shugaban na NCAA yana da digiri ta biyu (MSc) a fanin kasuwancin sufurin jiragen sama kuma yana daya daga cikin matukan jirage a tawagar shugaban kasa a matsayin Kyaftin.

A wani labari mai alaka da wannan, shugaban kasa ya kuma amince da nadin Mahmoud Sani Ben-Tukur a matsayin sabon wakilin dindindin ta Najeriya a Kungiyar ICAO.

Mista Oduadu ya ce, "Ben Tukur ya shafe fiye da shekaru 24 yana aiki fanoni daban-daban na sufurin jiragen sama kuma ya samu kwarewa da ilimi mai fadi kan tsaro da kulawa da kayayakin ayyuka na sashin na sufurin jiragen sama.

"Yana kuma da ilimi kan dokoki da yadda ICAO ke gudanar da ayyukanta da dokokin Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya."

Kafin nadinsa, shine mai bayar da shawara ga Ministan Sufurin Jiragen Sama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel