Fashola: Gwamnati za ta karasa manyan ayyukan da ta tattago kafin Buhari ya sauka
- Babatunde Raji Fashola SAN ya yi alkawarin kammala hanyar Abuja-Kaduna-Kano nan da 2023
- Ministan ya ce kafin Muhammadu Buhari ya tafi za a gama dagar Neja da hanyar Legas-Ibadan
- Ministar kudi ta bayyana shirin Gwamnatin tarayya na kashe har Naira tiriliyan 1.4 a kan ayyuka
FCT, Abuja - Ministan ayyuka na kasa, Babatunde Raji Fashola SAN ya ce za a gama titin Abuja-Kano, da na Legas-Ibadan da gadar Neja nan da watanni 12.
A ranar Talata, jaridar Leadership ta rahoto Ministan ayyukan yana mai wannan bayani a wajen wani taron ganawa da jama’a da aka shirya a garin Abuja.
Ma’aikatar yada labarai da raya al’adu ta hada wannan taro kamar yadda ta saba yi domin bayyana irin nasarorin da gwamnatin nan mai-ci ta samu.
Ministan ya ce ma’aikatarsa ta bada kwangilolin tituna 1, 018 na ayyuka 859 a jihohi 36 da garin Abuja. Jaridar nan ta Vanguard ta fitar da irin wannan rahoton.
Muhimman ayyuka 3
A cewar Ministan, gwamnatin tarayya za tayi kokari wajen ganin ta kammala duka wadannan manyan ayyuka kafin wa’adin Muhammadu Buhari ya cika.
Ana kokarin fadada titin Abuja-Kaduna-Kano wanda zai hada jihohin Arewacin Najeriya da birnin tarayya Abuja. A halin yanzu wannan aiki yana ta tafiya.

Asali: UGC
Baya ga haka akwai babban titin Legas zuwa Ibadan wanda an dade da fara aikin. Sai kuma gadar nan ta 2nd Niger wanda ta hada 'Yan Neja-Delta da kasar Ibo.
Shirin da muke yi a 2022 - Zainab Ahmed
A wajen wannan taro, Ministar kudi, kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, Zainab Ahmed ta samu damar yin jawabi, ta bayyana irin nasarorin da suka samu.
Zainab Ahmed ta ce gwamnatin tarayya ta fi maida hankali wajen kashe kudi a kan samar da abubuwan more rayuwa domin inganta tattalin arzikin kasa.
A wajen wannan taro, an ji cewa Najeriya za ta kashe kimanin Naira tiriliyan 1.42 a bana. Sannan gwamnati za a kashe Naira tiriliyan 2.11 wajen raya mutane.
EFCC v Okorocha
Dazu nan ku ka ji cewa hukumar EFCC ta fara samun nasara a kan Rochas Anayo Okorocha, Alkali ya bukaci a karbe wani gidan da ya mallaka a Abuja.
Hukumar EFCC ta na zargin cewa da kudin gwamnatin Imo aka saye gidan, don haka kotu ta ce a karbe gidan sai sun karkare shari’a a babban kotun tarayyar.
Asali: Legit.ng