Gwamnatin tarayya zata kwaso yan Najeriya dake zaune a kasar Ukraniya
- Ma'aikatar harkokin waje da hulda tsakanin gwamnatoci ta bayyana niyyar kwaso yan Najeriya dake Ukraniya
- Ministan harkoki ya ce tashin jirgi na da hadari yanzu saboda yakin da ake yi
- Yan Majalisar wakilan tarayya sun ce zasu tafi Ukraine kai tsaye don kwaso yan Najeriya dake wajen
Abuja - Gwamnatin tarayya ta sanar da shirin da take y na kwashe yan Najeriya dake zaune a Ukraniya sakamakon yakin da ya barke tsakanin kasar da Rasha a ranar Alhamis.
Gwamnati ta ce tana shirya jirgi na musamman da don kwaso su muddin aka bude tashohin jirgi.
Ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama, a hirar da yayi a tashar NTA yace an tuntubi ofishin jakadancin Najeriya dake Kiev kan shirya yadda za'a kwaso wadanda ke niyyar dawowa gida.
A cewarsa, har da wadanda ke cikin biranen Donestk da Luhensk, yankuna biyu da suka balle daga Ukraniya.
Ministan ya tabbatarwa yan Najeriya cewa za tay duk abinda zata iya don tabbatar da tsaron yan Najeriya, musamman dalibai.
Gwamnatin Buhari Ta Faɗa Wa Rasha Ta Janye Sojojinta Daga Ukraine
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta gana da wakilan kasashen G7 a Najeriya inda ta nuna damuwar ta game da rikicin Rasha da Ukraine tana mai kira da a warware lamarin cikin zaman lafiya, rahoto Daily Trust.
Ministan harkokin kasashen waje, Goeffrey Onyeama, ya gana da wakilan a ranar Juma'a a Abuja, yana mai cewa gwamatin Najeriya ta yi kira da a zauna lafiya kuma a yi amfani da diflomasiyya da wurin warware matsalar cikin lumana.
Onyeama ya ce Najeriya bata goyon bayan matakin da Rasha ta dauka na amfani da karfin soji, tana mai kira ga Rasha ta janye dakarunta, rahoton The Punch.
Asali: Legit.ng