Rashin wutan lantarki ya zama tarihi a Najeriya, Ministan Buhari
- Ma'aikatar labarai ta bayyana irin nasarorin da gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta samu cikin shekaru 6
- Karamin Ministan wutan lantarki yace yanzu ana samun wadataccen wuta kuma nan da karshen shekara kusan kowa zai samu
- Ministocin Buhari daban-daban sun bayyana nasarorin da ma'aikatunsu suka samu cikin yan shekarun nan
Abuja - Karamin Ministan makamashin Najeriya, Goddy Jedy Agba, ya bayyanawa yan Najeriya cewa rashin wutan lantarki ya zama tarihi a kasar.
Ministan ya bayyana hakan a taron da ma'aikatar labarai da al'adu ta shirya kan nasarorin da Gwamnatin Shugaba Buhari ta samu kan manyan ayyukan cigaba, rahoton TheCable.
Agba yace nan da karshen shekarar nan, kashi 85% na yan Najeriya zasu samu lantarki a banza.
Ministan yace gwamnatin tarayya na kokari wajen ganin kowani gida a Najeriya ya samu mita.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"Rashin wutan lantarki ya zama tarihi. Nan da karshen shekara kashi 85% na yan Najeriya zasu samu lantarki."
"Hakazalika dukkan gidaje zasu samu mita - kudin wutan da kaci kadai zaka biya."
Ya kara da cewa ayyukan lantarki da gwamnatin tarayya ta fara zasu kammala kafin karewar wa'adin shugaba Buhari.
Muna shirin karban sabon bashin $3bn don kammala wasu ayyuka 10, Ministar Kudi
A wani labarin kuwa, ministar kudi, kasafin kudi, da shirye-shiryen kasa, Zainab Ahmed, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya na shirin rattafa hannu kan sabon bashin $3.387 billion don yin wasu ayyuka 10 a fadin tarayya.
Ta ce gwamnatin Shugaba Buhari ya aiwatar da wasu manyan ayyukan da zasu amfani al'ummar Najeriya.
Tace:
"A 2022 kadai, muna shirin kashe N1.42 trillion kan manyan ayyuka kuma N2.11 trillion kan gina mutane."
Tace ayyukan da za'a aiwatar da sabon bashin sun hada da ginin layin dogon cikin birnin Kano, ginin titin garin Lafiya, jihar Nasarawa, fadada titin 9th Mile (Enugu)-Otukpo-Makurdi, dss.
Asali: Legit.ng