Mataimakin gwamnan Zamfara: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sanata Nasiha

Mataimakin gwamnan Zamfara: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sanata Nasiha

  • Bayan tsige mataimakin gwamnan Barista Aliyu Mahdi Gusau, an daura Sanata Muhammad Hassan Nasiha
  • Jama'a da dama na son sanin wanene wannan bawan Allahn da aka daura a kujera mafi daraja ta biyu a jihar ta Zamfara
  • Wannan yasa muka tattaro muku bayanai game da wannan sanatan da ya tsinci kansa a matsayin mataimakin gwamna

Zamfara - A yau ne aka tsige Mahdi Aliyu Gusau daga kujerar mataimakin gwamna, aka zaba tare da rantar Sanata Muhammad Hassan Nasiha a matsayin wanda ya maye gurgin Mahdi Gusai.

Mabiya Legit.ng Hausa za su so sanin bayanai kan wannan sanatan da aka ba mukamin mataimakin gwamnan rana tsaka.

Muhammad Hassan Nasiha ya zama mataimakin gwamna
Mataimakin gwamnan Zamfara: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da Sanata Nasiha | Hoto: @tvcnewsng
Asali: Twitter

Mun tattaro muku bayanai daga kafafe game da sanata Nasiha kamar haka:

1. Haihuwarsa

An haifi Sanata Nasiha a ranar 12 ga watan Disamban 1960, a yanzu yana da akalla shekaru 61 a duniya.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamna Matawalle ya rantsar da sabon mataimakinsa, ya tsokani Mahdi Gusau

2. Matakin karatunsa

Nasiha ya yi karatun difloma a fannin jinya da ungozoma kafin daga bisani ya kama aikin gwamnati gadan-gadan.

3. Ayyukansa da mukamansa

Bayanan da muka samo daga kafafe masu tushe sun ce, Nasiha ya rike mukaman kwamishina ma'aikatun lafiya, kasuwanci, muhalli, albarkatun ruwa, filaye da gine-gine, kananan hukumomi da masarautu duk a jihar Zamfara.

4. Shigarsa majalisa

Sanata Nasiha ya shiga majalisar dokokin tarayya a shekarar 2007, inda ya rike kwamitoci da dama.

Daga ciki, ya rike shugaban kwamitin kimiyya da fasaha, asusun gwamnati, sufurin jiragen ruwa, lafiya, iskar gas, samar da ayyukan yi da kwadago da dai sauransu.

5. Ya zama mataimakin gwamna

A yau 23 ga watan Fabrairu, sanata Nasiha ya zama mataimakin gwamnan Zamfara bayan tsige Barista Mahadi Aliyu Gusau. A yau din kuma gwamnan jihar, Bello Matawalle ya rantsar dashi.

Kara karanta wannan

Zamfara: Bayan tsige mataimakin gwamna, majalisa ta maye gurbinsa da sanata

Sai dai, abin tambayar, ya labarin zamansa Sanata take?

Gwamna Matawalle ya rantsar da sabon mataimakinsa, Sanata Nasiha

A tun farko kunji cewa, Gwamna Muhammad Bello Matawalle na jihar Zamfara ya rantsar da sabon Mataimakinsa, Sanata Hassan Nasiha.

Wannan dai na zuwa ne biyo bayan tsige tsohon mataimakin, Barista Aliyu Gusau, da kuma tantace sabon mataimakin da majaisar dokokin jihar ta gudanar yau Laraba.

Sanata Nasiha ya karbi shahadar fara aiki ne a wurin babbar alkalin jihar Zamfara, mai Shari'a Kulu Aliyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.