Da Dumi-Dumi: Kotu ta bada umarnin kwace kadarori 10, da kudaden Banki na tsohon gwamnan Zamfara
- Kotun tarayya a Abuja ta ba da izinin kwace kadarori kusan 10 da makudan kudin dake kwance a Banki mallakin Abdul'aziz Yari
- Alkalin Kotun ya ce umarnin na wucin gadi zai kwashe kwanaki 60, kuma bayan haka ICPC zata iya neman kwace su har abada
- A cewar hukumar yaƙi da cin hanci ICPC wasu daga cikin kadarorin na kasar Amurka wasu kuma na nan gida Najeriya
Abuja - Babbar Kotun tarayya dake zamanta a Abuja, ta bada umarnin wucin gadi na kwace kadarori kusan 10, da makudan kuɗin dake maƙare a Banki da ake zargin mallakin tsohon gwamna, Abdul'aziz Yari ne.
Mai shari'a Obiora Egwuatu, shi ne ya bada umarnin yayin yanke hukunci kan bukatar lauyan hukumar yaƙi da ayyukan cin hanci mai zaman kanta (ICPC), Osuobeni Ekoi Akponimisingha.
Alkalin Kotun ya ce umarnin na wucin gadi zai ɗauki tsawon watanni biyu ne kacal, kamar yadda Jaridar The Nation ta ruwaito.
Mai Shari'a Egwuatu ya kara da cewa Kotu ta ɗauki wannan matakin ne domin baiwa hukumar ICPC damar kammala bincikenta a tsanake.
Kazalika ya bayyana cewa bayan kammala bincike hukumar na da damar neman izinin kwace dukiyar baki ɗaya.
Alkalin ya umarci hukumar ICPC ta fitar da hukuncin Kotun ga al'umma domin duk wanda yake da sha'awa kan kadarorin ya yi bayanin dalilin rashin dacewar mallaka wa FG baki ɗayan su.
A cewar ICPC, wasu daga cikin kadarorin suna Maryland a ƙasar Amurka, Abuja, Kaduna da wasu garuruwa, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
Daga nan kuma sai Alkalin ya ɗage sauraron ƙarar har zuwa ranar 28 ga watan Afrilu, da za'a dawo domin tafka mahawara kan kwace dukiyar har abada.
A watan Janairun shekarar 2021, Hukumar ICPC ta samu nasarar kwace makudan kudi da suka kai dala $669,000 masu alaƙa da tsohon gwamnan.
Abu hudu da ya dace ku sani game da Mahdi Gusau
A wani labarin kuma mun tattaro muku jerin Muhimman abubuwa hudu da ya kamata ku sani game da Mahdi Aliyu da Majalisa ta tsige a Zamfara
A yau Laraba, 23 ga watan Fabrairu, 2022, majalisar dokokin jihar Zamfara ta tsige mataimakin gwamna, Barista Mahdi Aliyu Gusau.
Tun bayan sauya shekar gwamna Matawalle daga PDP zuwa APC, alaƙa tai tsami tsakanin su, mun tattaro muku abu hudu game da Gusau.
Asali: Legit.ng