Karya ne, ba'ayi gobara a ma'aikatar kudi ba, batir ne kawai ya kama da wuta: Ministar Kudi
1 - tsawon mintuna
- Mai magana da yawun Ministan kudi ya yi martani da labaran cewa ana gobarar a hedkwatar ma'aikatar kudi
- Najeriya ta waye gari da labarin yadda gobara ta fara cin ma'aikatar kudi dake birnin tarayya Abuja
- Ma'aikatar ta bayyana cewa wasu batura ne suka kone amma ba ma'aikatar bane ke kamawa da wuta ba
Abuja - Ma'aikatar kudin Najeriya ta yi watsi da labaran cewa hedkwatarta dake birnin tarayya Abuja ya kama da wuta da safiyar Laraba, 23 ga watan Febrairu, 2022.
Yunusa Tanko Abdullahi, mai magana da yawun Ministar kudi, Zainab Ahmed Shamsuna, ya bayyana haka a jawabin da ya saki a shafin hukumar na Facebook.
Tanko Abdullahi yace wani batur ne kawai ya kama da wuta kuma da wuri aka kashe wutan.
Yace:
"Hedkwatar Ma'aikatar kudin tarayya bai kama da wuta ba kamar yadda ake yadawa a kafafen sada zumunta. Kawai wani abu ya faru a ginin kasa na wani batir kuma tuni jami'an tsaro suka kashe."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Premium Times ta ruwaito cewa jami'an kwana-kwana sun dira ma'aikatar domin kashe wutan amma aka je su tafi ba'a bukatarsu.
Jami'an dake gaban ma'aikatar sun ce babu wuta saboda haka su juya
Asali: Legit.ng
Tags: