Da duminsa: Jami'an tsaro sun damke Omoyele Sowore, an kaishi Abbatoir
- Bayan watanni da shan iskan yanci, jami'an tsaro sun sake damke shahrarren dan fafutuka Omoyele Sowore
- Abokansa sun bayyana cewa har yanzu basu san dalilin da ya sa suka damkeshi ba
- Sowore a baya ya kwashe kusan shekara guda tsare hannun hukumar DSS kafin aka sake shi
Abuja - Dan fafutuka kuma tsohon dan takaran kujeran shugaban kasa, Omoyele Sowore, ya shiga hannun jami'an tsaro ranar Alhamis, 24 ga watan Febrairu, 2022 a Abuja.
Kakakin jam'iyyar African Action Congress AAC, Femi Adeyeye, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki.
Yace jami'an tsaron sun damke Sowore ne yana fitowa daga kotu a unguwar Gudu dake birnin tarayya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yace:
"Muna fitowa daga kotu inda Shugaban jam'iyya, jigogi da mambobi suka halarci zaman kotu kan karar da aka shigar kan INEC da masu kokarin kwace jam'iyyar."
"Kawo yanzu da muka saki wannan jawabi yana rike hannun ofishin SARS da ake kira Abattoir kuma jami'an ofishin suka damkeshi."
Sowore, wanda shine mammalakin gidan jaridan Sahara Reporters, ya daukaka kara kan hukuncin kotun da ta baiwa Leonard Nzenwa shugabannin jam'iyyar AAC.
Shari'ar Nnamdi Kanu: Mai gidan jaridar Sahara Reporters ya gamu da fushin 'yan sanda
Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya sun tarwatsa taron su Omoyele Sowore da wasu mutane da suka halarci babbar kotun tarayya don ganin yadda ta kaya a gurfanar da shugaban 'yan IPOB, Nnamdi Kanu, Punch ta ruwaito..
An ruwaito cewa Sowore wanda ya isa babbar kotun tarayya da ke Abuja a safiyar ranar Laraba an hana shi shiga harabar kotun kuma wasu ‘yan daba ne suka kai masa hari.
Bayan haka ne Jami'an Tsaro suka fara harba harsasai a iska wanda ya haifar da fargaba da rudani.
Asali: Legit.ng