Dalilin da yasa Gwamnatin Buhari ba zata yi tattaunawar sulhu da yan bindiga ba, Minista ya fasa kwai
- Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ba zata taba tsoma hannu a tattaunawar sulhu da yan bindiga ba saboda wasu dalilai
- Ministan yada labarai da al'adu na ƙasa, Lai Muhammad, yace lamarin yan bindiga yana da matukar rikitarwa
- Ya ce akwai ayyukan da gwamnati ke yi na kawo karshen matsalar ta bayan fage, ba tare da kowa ya sani ba
Abuja - Minsitan labarai da al'adu, Alhaji Lai Muhammad, yace gwamnatin tarayya ba zata tsoma hannu cikin tattaunawar sulhu da yan bindiga ba.
Minsitan ya yi wannan magana ne yayin da yake fira da Jaridar Daily Trust ranar Litinin 21 ga watan Fabrairu, 2022.
Yace saboda rashin tabbas da rikitarwar lamarin, kamata ya yi a bar gwamnatin jihohi su ɗauki matakin sulhu ko akasin haka da kan su.
Karin Bayani: 'Bama-baman' da yan bindiga suka ɗana sun tashi da rayukan dandazon Mutane a jihar Neja
A jawabinsa Lai ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Sha'anin yan bindiga lamari ne mai rikitarwa. Idan zaku iya tuna wa, wasu gwamnoni sun kama hanyar tattaunawa da ƴan bindiga da farko, amma daga baya suka jefar da lamarin."
"Wani lokaci zasu amince idan aka ba su wani adadi na kuɗi zasu bar ayyukan ta'addanci, amma idan an ba su sai kuma su yi amfani da shi su siyo makamai."
"Shiyasa FG ta bar jihohi su yanke zasu yi sulhu da su yan ta'adda ko kuma ba za su yi ba, gwamnatin tarayya ta tsame hannun ta."
Akwai abubuwa da dama da bamu bayyana wa - Minista
Lai Muhammad ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na aiki tukuru wajen kawo karshen matsalar ba tare da ta bayyana ba, musamman game da mika wuyan yan ta'adda.
"Akwai abubuwan dake faruwa ta bayan fage ba tare da mun sanar ba, yan bindiga na miƙa wuya. Idan kuka duba lamarin Boko Haram kusan mutum 30,000 sun miƙa wuya."
"Wasu mun bayyana wa yan Najeriya, amma musamman shugabannin su ba mu faɗi ba, saboda idan mun bayyana za'a iya samun matsala. Muna yin komai dan kawo zaman lafiya."
A wani labarin da daban kuma Majalisa ta tsige mataimakin shugaba, wasu yan majalisu biyu sun yi murabus
Majalisar dokokin jihar Ebonyi ta bayyana murabus ɗin mataimakin kakaki da wasu mambobinta biyu a zaman Litinin.
Sai dai lamarin ya tada hatsaniya, yayin da mutanen uku baki ɗaya suka musanta ikirarin majalisa, suna nan daram a matsayin su.
Asali: Legit.ng