Sakamakon zirga-zirgar Buhari: Kasar Ingila ta narka Naira Biliyan 5 domin inganta wuta
- An cin ma yarjejeniya cewa gwamnatin Birtaniya za ta ba Najeriya gudumuwar Dala miliyan £10
- Za ayi amfani da wadannan kudi domin a tabbatar da shirin COP26 da aka shigo da shi a kasar nan
- Baya ga haka, an sa hannu a wata MoU da za su sa Dala £210,000 su shigo cikin asusun Najeriya
UK - Birtaniya ta sa fam miliyan £10 cikin wani aiki da Najeriya take yi domin a rage fitar da hayakin sinadarin Carbon. This Day ta fitar da wannan rahoto.
Gwamnatin Ingila ta bada wadannan makudan kudi ne da nufin rage iskar carbon, sannan kuma a tabbatar an gyara wuta, a kuma goyi bayan shirin nan na COP26.
Rahoton da Sun ta fitar ya bayyana cewa Ingila da Ireland sun rattaba hannu a yarjejeniyar da za ta taimakawa gwamnatin Najeriya wajen yaki da rashin gaskiya.
Ministan harkokin Afrika na kasar Ingila, Vicky Ford da Ministan shari’an Najeriya, Abubakar Malami suka sa hannu a wannan yarjejeniya ta MoU a makon nan.
Sakataren din-din-din na ma’aikatar shari’ar kasar, Mohammed Umar ya wakilci Malami SAN.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Kasashen biyu sun sha alwashin hada-kai domin yakar sata da safarar kudi, damfara da sauran rashin gaskiya irinsu karbar cin hanci da rashawa da ake yi.
Ford ta ce tun a wajen wani taro da aka yi kwanaki, hukumomin Ingila da na Najeriya sun sha alwashin kokari wajen ganin kawo karshen satar kudin al’umma.
FG za ta samu £210, 000
Kasar Turan ta sa hannu a wata yarjejeniya da gwamnatin tarayya da za ta bada dama a aiko mata £210,610 a sakamakon wani binciken satar kudi da aka yi.
Za a biya kasar wannan kudi ne bayan wani dogon bincike da ofishin SFO ta yi shekaru hudu tana yi. Nan da kwanaki 28 ake sa ran kudin za su shigo asusun kasar.
Gwamnatin Muhammadu Buhari ta yi alkawari cewa za tayi amfani da wannan kudi (kusan Naira miliyan 120) da za a biya kan ayyukan da za su taimaki jama’a.
Taron ECOWAS a Legas
A jiya aka ji tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya ce zaben 2023 zai zama mai inganci da nagarta, duk da irin barazanar da ake fuskanta a yau.
Dr. Goodluck Ebele Jonathan ya na ganin rikici ba zai barke a zaben da za ayi a shekarar badi ba, ko da cewa ana fama da rashin tsaro a wasu wurare a kasar nan.
Asali: Legit.ng