Magabatan Yarabawa za su ba ka nasarar zama shugaban kasa, Alaafin ga Tinubu
- Babban basarake mai daraja ta daya a Oyo, Oba Lamidi Olayiwola, ya sanar da cewa ya na da tabbacin magabatan Yarabawa za su bai wa Tinubu nasara
- A cewar babban basaraken da ake kira da Alaafin na Oyo, ya ce ya na hango nasarar shugabancin kasa a tattare da Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas
- A yau Lahadi ne Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci fadar basaraken inda suka shiga ganawar sirrin da har yanzu ba a san abinda suka tattauna a kai ba
Alaafin na Oyo, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi a ranar Lahadi, ya ce ya na da tabbacin cewa magabatan Yarabawa za su bai wa jigon jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu nasarar zama shugaban kasar Najeriya a 2023.
Daily Trust ta ruwaitoo cewa, Sanata Tinubu ya ziyarci basaraken mai daraja ta farko na kasar Yarabawa a fadarsa da ke Oyo a ranar Lahadi.
Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, su biyun sun shige ganawar sirri bayan da tsohon gwamnan jihar Legas din ya isa fadar babban basaraken.
Jigon jam'iyyar APC din har a halin yanzu bai zanta da manema labarai ba kan abinda ya kai shi masarautar duk da an sakankance cewa ya je neman goyon bayan basaraken ne wurin neman kujerar shugabancin kasar Najeriya a zabe mai zuwa.
Tinubu, wanda ya ke daya daga cikin masu son nasarar samun tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyya mai mulki a zabe mai zuwa, ya sanar da burin hakan a wataan Janairu bayan da ya ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari domin bayyana shirinsa na takarar shugabancin kasan.
2023: Tinubu ya naɗa ɗan shekaru 31 a matsayin shugaban watsa labaransa na ƙasa
A wani labari na daban, yayin da zaben shugaban kasa na 2023 yake karatowa, babban jagoran APC kuma mai neman takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya nada wani matashi dan asalin Jihar Borno, Kwamared Muhammad Mahmud a matsayin shugaban watsa labaransa na kasa, Vanguard ta ruwaito.
Yayin tattaunawa da manema labarai a Maiduguri, Mahmud ya ce zai tabbatar ya janyo hankalin mutane kwan su da kwarkwata wurin ganin sun ba Jagaban goyon baya don maye gurbin Shugaba Muhammadu Buhari da kuma dasawa daga ayyukan da ya tsaya na ci gaban kasa.
Mahmud ya ce nadin nasa bai ba shi mamaki ba saboda ya yarda da salon mulkin Tinubu wanda ba ya nuna bambancin yanki ko kabila.
Asali: Legit.ng